COAS: Rundunar Sojin Najeriya Ta Nada Mukaddashin Hafsan Sojoji, Ta Bayyana Dalili
- Rundunar sojin Najeriya ta nada Abdulsalami Bagudu a matsayin Hafsan sojin kasa da Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ke hutu
- Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 20 ga Oktoba
- Bagudu, wanda ke rike da mukamin shugaban tsare-tsare, zai tafiyar da harkokin rundunar sojojin har zuwa dawowar Lagbaja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja — Rundunar sojin Najeriya ta sanar da Abdulsalami Bagudu a matsayin mukaddashin hafsan sojin kasa yayin da Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ke hutu.
Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba.
An nada mukaddashin hafsan soji
Nadin Bagudu a matsayin hafsan soji na riko na tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan rundunar a lokacin da Lagbaja ba ya nan, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Bagudu shi ne shugaban sashen tsare-tsare na rundunar sojin kasa.
A cewar Manjo Janar Nwachukwu:
"Bari mu yi bayani dalla dalla, an kafa rundunar sojin kasa bisa wani tsari da mai karfi wanda ya tanadi matakai na warware duk wata matsala da za a iya fuskanta.
"Kafin tafiya, an bi wasu matakai da suka dace domin shugaban sashen tsare-tsare (sojin kasa), Manjo Janar Abdulsalami Bagudu ya yi aiki a matsayin mukaddashin COAS yayin da ba ya nan."
Karanta labarai masu alaka da sojoji
Ana yada cewa hafsan sojoji na fama da rashin lafiya, an fara neman kujerarsa
Shugaban sojojin Najeriya ya ajiye aiki karkashin Tinubu? Bayanai sun fito
Rundunar sojoji ta faɗi matsayarta kan kiran kifar da gwamnatin Tinubu
Laftanar Janar Lagbaja ya rasu?
A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya na karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa hafsan sojojin kasar nan, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya rasu.
Rundunar ta ce kwata-kwata babu kamshin gaskiya a cikin labarin da ake yadawa na mutuwar Lagbaja wanda ta ce ya dauki hutu daga aiki a halin yanzu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng