'Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami'in Gwamnati da Mutane Masu Yawa a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Sace Babban Jami'in Gwamnati da Mutane Masu Yawa a Zamfara

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau a jihar Zamfara a ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoban 2024
  • A yayin harin, ƴan bindigan sun hallaka mutum biyu sannan suka yi garkuwa da matafiya masu yawa zuwa cikin daji
  • Daga cikin mutanen da aka sace har da jagoran hukumar RMAFC na Zamfara wanda yake kan hanyar zuwa birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da jagoran hukumar tattara kuɗin shiga da kasafin kuɗi (RMAFC) na jihar Zamfara, Alhaji Bashir Abara Gummi.

Ƴan bindigan sun yi awon gaba da Alhaji Bashir ne tare da mutane da dama a hanyar Funtua zuwa Gusau.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bayyana babban abin da ke barazana ga tsaron Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara
'Yan bindiga sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan bindiga sun tare hanya a Zamfara

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan bindigan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau ne a ranar Lahadi, inda suka farmaki motoci ciki har da motar da Alhaji Bashir ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Bashir Gummi, kamar yadda majiyoyi daga hukumar suka bayyana, yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja ne domin wani aiki lokacin da lamarin ya faru.

Yadda aka sace matafiya a jihar Zamfara

Wata majiya daga jami’an tsaro da ke da masaniya kan lamarin ta ce ƴan bindigan sun buɗe wuta kan motoci, suka kashe mutane biyu nan take kafin su yi garkuwa da Alhaji Bashir da sauran matafiya masu yawa.

"Ƴan bindigan sun tare hanya kuma abin takaici wasu motocin sun faɗa tarkonsu. Sun buɗe wuta kan motocin tare da sace matafiya da dama."

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun sojoji sun cafke ƙasurgumin ɗan bindiga, sun hallaka wasu kusan 100

- Wata majiya

Jaridar Leadership ta ce babban mai binciken kuɗi na jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Dan Maliki, ya tsallake rijiya da baya a yayin harin inda ya samu ya tsira daga inda ƴan bindigan suke.

Sojoji sun kashe ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun sake samun gagagarumar nasara a ƙoƙarin da suke yi na kakkaɓe ƴan ta'adda a Arewa maso Yamma.

Dakarun sojin da ke atisayen Hadarin Daji a jihar Zamfara sun kashe hatsabiban ƴan bindiga biyar a wani artabu da suka yi a safiyar ranar Laraba, 16 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng