Musulmai Sun Magantu kan Zargin Shirin Rushe Masallacin Juma'a, Sun ba Gwamna Shawara
- Kungiyar Kuteb Muslim Development Association (KMDA) ta yi magana kan zargin shirin rushe masallacin Juma'a
- Kungiyar ta yi Allah wadai da shirin rushe masallacin Juma'a a karamar hukumar Takum da ke jihar
- Legit Hausa ta yi magana da wani mazaunin Takum kan halin da ake ciki game da zargin rushe masallacin Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Taraba - Kungiyar Musulmai ta yi martani kan zargin shirin rusa babban masallacin Juma'a a jihar Taraba.
Kungiyar Kuteb Muslim Development Association (KMDA) a karamar hukumar Takum ta yi Allah wadai da lamarin.
Ƙungiya ta magantu kan zargin rushe masallaci
Shugaban kungiyar, Alhaji Bako Mairiga shi ya bayyana haka a yau Lahadi 20 ga watan Oktoban 2024 a Jalingo, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mairiga ya ce zargin shirin rushe babban masallacin Juma'a a Takum karan-tsaye ne ga Musulman Kuteb.
Ya ce gari irin Takum da ya sha fama da rikice-rikice a baya bai kamata a sake jefa shi matsala da tashin hankali ba.
Kungiyar Musulmai ta shawarci Gwamna Agbu Kefas
Kungiyar ta bukaci Gwamna Agbu Kefas da ya tabbatar ba a cigaba da shirin rushe masallacin ba domin samun zaman lafiya.
"Ukwe Ahmadu a matsayinsa na Musulmi ya ga dacewar gina masallacin Juma'a kusa da fada a shekarar 1912 saboda shi da sauran Musulmai su yi ibada a wurin."
"A matsayinmu na kungiya masu son zaman lafiya muna ganin rushe masallacin da fadar Takum zai kawo rudani da tashin hankali."
- Alhaji Bako Mairiga
Kungiyar ta kuma musanta zargin cewa Kuteb sun rusa masallaci da kuma hallaka wasu daga cikin masallata.
Legit Hausa ta tattauna da wani mazaunin Takum
Legit Hausa ta yi magana da wani mazaunin Takum kan halin da ake ciki game da zargin rushe masallacin Juma'a.
Abdulrahman Adamu ya tabbatar da cewa tabbas akwai kanshin gaskiya kan zargin rushe masallacin da ake yi.
Sai dai ya ce a yanzu an dauki mataki mai tsauri kuma maganar ta yi shiru zuwa yanzu babu wani shiri kan haka.
Gwamna ya musanta shirin rushe masallacin Juma'a
Kun ji cewa Gwamnatin jihar Taraba ta musanta zargin cewa ta na shirin rusa fadar Takum da babban Masallacin Juma'a a garin.
Kwamishinar yaɗa labarai, Zainab Usman Jalingo ta ce zargin ba shi da tushe, inda ta bukaci mutane su yi watsi da shi.
Tun farko dai kungiyar Kuteb ta Najeriya watau KYN ta zargi gwamnatin Agbu Kefas da yunkurin rusa wuraren na tarihi.
Asali: Legit.ng