Tochukwu: Abubuwa 5 game da Ɗan Kabilar Ibo da Ya Zama Limamin Masallacin Abuja
Abuja - Farfesa Iliyasu Usman, dan kabilar Igbo na farko da aka nada a matsayin limamin babban masallacin Abuja, ya gabatar da hudubarsa ta farko a ranar Juma’a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
An rahoto cewa nadin Farfesa Iliyasu a matsayin daya daga cikin limamai na babban masallacin kasa ya jawo kalaman yabo daga jama'a musamman kungiyar SEMON.
Jaridar Tribune Online ta bayyana abubuwa biyar da ya kamata a sani game da sabon limamin babban masallacin Juma'ar na Abuja.
1. Farfesan Larabci na farko daga Ibo
Farfesa Illyas ne farfesan Larabci na farko daga kasar Ibo, wanda ya bayyana irin nasarorin da ya samu a fannin ilimi da kuma gudunmawar da ya bayar ga ilimin addinin Musulunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Ya shiga tawagar limamai
Farfesa Illyas ya shiga sahun limaman masallacin Abuja da ke jagoranci a yanzu; Farfesa Ibrahim Makari da Farfesa Muhammad Kabir.
Kasancewar a yanzu limamin masallacin na hudu Sheikh Ahmad Onilewura yana jinya, limaman uku ne za su rika jagorantar sallar Juma'a da Khamsus Salawati biyar.
3. Ya samu goyon bayan SEMON
Kungiyar Musulmin Kudu Maso Gabashin Najeriya (SEMON) ta goyi bayan nadin Farfesa Illyas matsayin limamin babban masallacin Abuja.
Jaridar Aminiya, ta rahoto SEMON a wata sanarwa da ta fitar ta ce:
"Wannan gagarumin matsayi ba sheda ce ta sadaukar da kai da kwazonka na ilimi kadai ba, wani nauyi ne da ya rataya a wuyanka na jagorantar al'umma zuwa ga bautar Allah."
4. Tauraron hadin kan al'ummar Musulmi
Da dama na kallon Farfesa Illyas a matsayin tauraro wanda nadinsa ya zama wata shaida da ke nuna hadin kan al'ummar Musulmi tare da kore wariya ta kabilanci.
Mutane sun yabawa majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya NSCIA karkashin sarkin musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar kan wannan nadi.
5. Hudubarsa ta farko
Bayan nadin nasa, Farfesa Ilyas Usman ya gabatar da hudubarsa ta farko a matsayin daya daga cikin Limamin Masallacin kasa a ranar 18 ga Oktoba 2024.
An nada dan ibo limamin Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa mahukunta sun amince da nadin Farfesa Iliyasu Usman a matsayin sabon limanin babban masallacin Juma'a na Abuja.
Farfesa Iliyasu Usman ya shiga tarihin wannan masallaci, inda ya zamo dan kabilar Ibo na farko da ya rike mukamin babban limamin masallacin.
Asali: Legit.ng