PDP Ta Bayyana Matsayarta bayan APC Ta Lashe Zaben Ciyamomi a Kaduna

PDP Ta Bayyana Matsayarta bayan APC Ta Lashe Zaben Ciyamomi a Kaduna

  • Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Kaduna
  • Shugaban PDP na jihar, Edward Masha ya yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen wanda jam'iyyar APC ta lashe
  • Ya ƙara da cewa za su ƙalubalanci sakamakon zaɓen a gaban kotu domin ba za su amince da shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shugaban jam’iyyar PDP na Kaduna, Edward Masha, ya yi martani kan sakamakon zaɓen ciyamomin da aka gudanar a jihar.

Edward Masha ya yi zargin cewa an tafka kura-kurai a zaɓen kananan hukumomin wanda aka gudanar a ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.

PDP ta yi zargin magudi a zaben Kaduna
PDP za ta kalubalanci zaben ciyamomin Kaduna a kotu Hoto: @AliyuSaidTahir2
Asali: Twitter

PDP ta yi fatali da zaɓen ciyamomin Kaduna

Kara karanta wannan

Kaduna: APC ta lallasa PDP da sauran jam'iyyun adawa a zaben ciyamomi

Jaridar The Punch ta ce Edward Masha wanda tsohon kwamishinan albarkatun ruwa ne a Kaduna ya bayyana hakan ne yayin da ganawa da manema labarai kan sakamakon zaɓen wanda APC ta lashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na PDP ya yi zargin cewa an cire wasu muhimman kayyayaki, musamman takardun sakamakon zaɓe a mazaɓu da ƙananan hukumomi.

"SIECOM ta gayyace mu domin karɓar muhimman kayayyaki daga babban bankin Najeriya, amma da muka duba sai muka gano cewa babu takardun sakamakon zaɓe."

"Cire takardun da aka yi ya sanya zaɓen ya zama ba sahihi ba, kuma wakilanmu sun tsaya tsayin daka wajen kin yarda da murɗiya."

- Edward Masha

Shugaban PDP ya zargi APC da yin maguɗi

Masha ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da kashe dimokaradiyya da kuma zagon ƙasa ga tsarin zaɓe.

Ya jaddada cewa jam’iyyar PDP za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen a gaban kotu sannan kuma za ta ci gaba da nemawa jama'a adalci.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya feɗe gaskiya kan rigimar shugabancin PDP na ƙasa

"Ba za mu yarda da wannan murɗiyar ba. Ba za mu yarda da kashe dimokradiyya ba. Za mu ƙalubalanci wannan sakamakon a kotu, kuma za mu ci gaba da neman adalci ga mutanenmu.”

- Edward Masha

APC ta lashe zaɓe a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC ta lashe zaɓe a dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

Jam'iyyar APC ta kuma lashe kujerun kansiloli 255 a zaɓen ƙananan hukumomin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kaduna (KAD-SIECOM) ta gudanar ranar Asabar, 19 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng