An Shiga Tashin Hankali a Abuja, 'Yan Ta'adda Sun Kashe Babban Jami'in Gwamnati
- An shiga tashin hankali a karamar hukumar Bwari da ke Abuja yayin da aka kashe shugaban wata cibiyar gyaran tarbiyya
- Rahotanni sun nuna cewa wani dan ta'adda da ba a san ko wanene ba ne ya kashe Bala Tsoho Musa da daren Juma'a da katako
- Jami’in ’yan sanda mai kula da Bwari, CSP Babayola Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana kan yin bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani dan ta'adda da har yanzu ba a gano ko wanene ba ya kashe shugaban cibiyar gyaran tarbiyya ta Abuja, Bala Tsoho Musa.
An tsinci gawar Bala Musa wanda aka fi sani da kwamared a daren Juma’a a cikin cibiyar da ke Kuchiko, wani gari da ke karamar hukumar Bwari a Abuja.
Abuja: An kashe jami'in gwamnati
Hukumar kula da babban birnin tarayya (FCTA) ce ta kafa cibiyar gyaran tarbiyyar, kamar yadda rahoton TrustTVNews ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce hukumar FCTA ta kafa cibiyar domin horar da mabarata da sauran mutanen da aka kama a yankin saboda wata matsala da ta shafi jama’a.
"Wani mahari da har yanzu ba a gano ko wanene ba ya kashe shugaban cibiyar gyaran tarbiyya ta Abuja, Bala Tsoho Musa."
- A cewar rahoton.
Majiyoyin da suka zanta da manema labarai a ranar Asabar sun bayyana cewa an tsinci gawar marigayin a kan keken guragunsa.
Yadda aka tsinci gawar jami'in gwamnatin
Daya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa an gano wani katako da ake kyautata zaton da shi aka yi amfani wajen kashe jami'in, yayin da aka nemi wayoyinsa biyu aka rasa.
Majiyar ta ce:
“Babu wani daga gidan marigayin da ya san faruwar lamarin, watakila saboda karar na’urar samar da wutar lantarki da ke a wurin."
"Har sai da wata kurma wacce ta kan taimaka wa iyalansa a matsayin 'yar aiki ta ankarar da mutane abin da ta gani a kan hanyarta ta komawa masauki,” a cewar majiyar.
Da aka tuntubi jami’in ’yan sanda mai kula da Bwari, CSP Babayola Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana kan bincike.
An kai 'yan kwaya gidan gyaran tarbiya
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NDLEA ya bayyana samun gagarumar nasarar kama mutane 319 da ake zargi da ta'ammalli da miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan hukumar reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ya ce an kai 'yan kwaya 26 gidan gyara tarbiyya yayin da ta gurfanar da wasu gaban kotu.
Asali: Legit.ng