Nnamdi Kanu: Kotu Ta Yi Barazanar Tura Shugaban DSS Gidan Yari, An Gano Dalili

Nnamdi Kanu: Kotu Ta Yi Barazanar Tura Shugaban DSS Gidan Yari, An Gano Dalili

  • An gargadi hukumar tsaro ta farin kaya, DSS kan take hakkin shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da ake tsare da shi
  • Babbar Kotun Tarayya ta tura gargadin ga shugaban hukumar kan kin ba lauyoyin Kanu ganawa da shi kwanaki uku duk mako
  • Hakan ya biyo bayan zargin da lauyoyinsa suka yi na cewa hukumar DSS tana hana su ganawa da Kanu da ake zargi da ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta gargadi shugaban hukumar DSS kan shari'ar mai fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Kotun ta yi barazanar garkame shugaban DSS, Adeola Ajayi kan kin ba Kanu damar ganawa da lauyoyinsa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Kotu ta yi barazanar tura shugaban DSS gidan yari kan Nnamdi Kanu
Kotu ta gargadi shugaban DSS kan dakile hakkokin Nnamdi Kanu. Hoto: Aloy Ejimakor.
Asali: Facebook

Zargin da ake yiwa Nnamdi Kanu

Premium Times ta ruwaito cewa ana zargin shugaban IPOB masu rajin kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu da ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kanu na garkame a Najeriya tun bayan dawo da shi kasar daga Kenya a watan Yunin shekarar 2021.

A watan Mayun 2024, Mai Shari'a, Binta Nyako ta umarci DSS ta ba lauyoyin Kanu damar ganawa da shi, Sahara Reporters ta ruwaito.

Nnamdi Kanu: Kotu ta gargadi shugaban DSS

Nyako ta ba da umarnin ne inda ta ce lauyoyin za su na ganawa da Kanu har kwanaki uku a cikin mako.

"Muna baka umarni ka bi dokar da muka gindaya na ba lauyoyin Kanu damar ganawa da shi a ranakun Litinin da Laraba da Juma'a a cikin mako."
"Saba wannan umarni zai tilasta kotu zarginka da kin bin dokarta wanda zai kai ka ga zuwa gidan yari ba tare da bata lokaci ba."

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

- Sanarwar kotun

Gwamnoni sun bukaci sakin Nnamdi Kanu

Kun ji cewa Ƙungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Gabas sun gana a jihar Enugu domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi yankin na su.

Gwamnonin a yayin ganawar ta su sun cimma matsayar za su gana da shugaban ƙasa kan ƙalubalen matsalar rashin tsaron da ke addabar yankin.

Sun kuma yanke shawarar cewa za su buƙaci a saki shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu wanda ke fuskantar tuhumar ta'addanci a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.