Bayan Kara Kudin Fetur, Tinubu Ya Shirya Kakabawa 'Yan Najeriya wani Sabon Haraji

Bayan Kara Kudin Fetur, Tinubu Ya Shirya Kakabawa 'Yan Najeriya wani Sabon Haraji

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shirya sanya harajin kaso biyar ga dukkanin ayyukan sadarwa, wasanni da nau'ukan caca
  • Wannan dai na kunshe ne a cikin sabon kudirin da gwamnatin ta gabatar wanda zai yi garambawul ga tsarin harajin Najeriya
  • 'Yan Najeriya za su shirya biyan sabon harajin kashi biyar yayin da suka buga waya, saka data, yin wasanni a intanet ko buga caca

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya kakaba harajin kashi biyar kan kiran waya, data da sauran ayyukan sadarwa, wasanni, caca da sauransu.

Bullo da sabon harajin na daga cikin wani bangare na sabon kudirin dokar da gwamnatin za ta gabatar na yin garambawul ga tsarin harajin Najeriya.

Kara karanta wannan

Direbobin da ke bin babbar hanya a Arewa za su fara biyan haraji a sabon tsari

Gwamnatin tarayya na shirin kakaba haraji a sadarwa, wasanni da caca
Gwamnatin Najeriya ta sanya karin haraji a sadarwa, wasanni da caca a sabuwar doka. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Kudirin dokar na dauke ne da kwanan wata 4 ga Oktoba, 2024 kuma an same shi daga majalisar dokokin kasar kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sanyawa sadarwa sabon haraji

Wani bincike kan kudurin da aka gabatar a ranar Juma’a ya nuna cewa ana neman bullo da haraji kan wayar tarho, wasanni da nau'ikan caca da ake yi a Najeriya.

Wani sashe na kudurin na cewa:

"Yawan ma'amalar da aka yi zai samar da kimar da kamfanoni za su rika caja daga abokan huldarsu walau a tsarin kudi ko wani abu na kimar kudin ko kuma duka biyun.
“Za a fara fitar da haraji kan ayyukan da suka hada da sadarwa, wasanni, caca, yin fare, da sauran nau'ikan caca wanda ake gudanarwa a Najeriya."

Yadda harajin zai shafi 'yan kasa

Tsarin harajin da ke cikin kudirin ya nuna cewa za a kakaba harajin kashi biyar na ayyukan sadarwa da hukumar sadarwa ta Najeriya ta ke kula da su.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Jaridar This Day ta rahoto cewa, 'yan Najeriya za su biya harajin kashi biyar yayin da suka buga wasanni a intanet da sauran nau'ikan caca.

Sabon tsarin harajin ya kasance wani bangare na dabarun gwamnati na bunkasa kudaden shiga da ba na mai ba yayin da kasar ke fama da matsi na kasafin kudi.

NNPC ya kara kudin man fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin man Najeriya (NNPCL) ya kara farashin man fetur a gidajen mai mallakinsa da ke Abuja da wasu jihohi.

Farashin man ya tashi zuwa N1,030 kan kowace lita a gidajen mai na kamfanin NNPCL da ke Abuja a ranar Laraba, 9 ga watan Oktobar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.