Jigawa: Gwamnonin Arewa Sun ba da Mamaki, Sun Tallafa da Miliyoyi bayan Iftila'i

Jigawa: Gwamnonin Arewa Sun ba da Mamaki, Sun Tallafa da Miliyoyi bayan Iftila'i

  • Yayin da ake cigaba da jimamin rasa rayuka a jihar Jigawa, gwamnonin Arewacin Najeriya sun ba da tallafi mai tsoka
  • Shugaban gwamnonin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jajantawa gwamnatin jihar da al'umma kan wannan iftila'i da ya afku
  • Gwamna Inuwa ya ce domin ragewa waɗanda abin ya shafa radadi, kowane gwamna a yankin zai ba da gudunmawar N50m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Jigawa - Gwamnonin jihohin Arewa sun yi abin a yaba bayan iftila'in da ya faru a jihar Jigawa.

Kowane gwamna da ke yankin ya ba da gudunmawar N50m domin tallafawa wadanda iftila'in ya shafa.

Gwamnonin Arewa sun tallafa da makudan kudi a jihar Jigawa
Gwamnonin Arewacin Najeriya sun ba tallafin makudan kudi saboda iftila'in da ya faru a jihar Jigawa. Hoto: Ismaila Uba Misilli.
Asali: Facebook

Gwamnonin Arewa sun tallafa kan iftila'in Jigawa

Kara karanta wannan

Gwamna Ya kere tsara, ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi sama da N80,000

Sakataren yada labaran Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook a daren jiya Asabar 19 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Misilli ya ce Gwamna Inuwa wanda ya jagoranci tawagar ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Inuwa wanda shi ne shugaban gwamnonin Arewa ya ce kowace jiha a yankin za ta ba da gudunmawar N50m saboda tallafawa.

Gwamna Inuwa ya fadi tasirin iftila'in gare su

Gwamnan ya bayyana muhimmancin hadin kai wurin ba da tallafin domin taimakawa wadanda abin ya shafa.

"Wannan iftila'i ya shafe mu gaba daya, dole za mu tallafawa al'umma da gwamnatin jihar Jigawa kan wannan lamari da ya afku."
"Wannan rashi ba iya Jigawa ba ne, ya shafi yankin Arewa da ma kasa baki daya, abin takaici ne rasa irin wadannan matasa a kasa."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya ciri tuta, ya sanar da sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata

- Gwamna Inuwa Yahaya

Gwamna Inuwa zai biya albashin N70,000

Kun ji cewa A karshe, Gwamnan Muhammadu Inuwa Yahaya ya amince da fara biyan mafi karancin albashi N70,000 a Oktoban shekarar 2024.

Gwamnan ya sanar da haka ne a ranar Alhamis 10 ga watan Oktoban 2024 bayan a baya ya ce ba zai iya biyan mafi ƙarancin albashin ba a jihar.

Mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kamitin sabon albashin, Dakta Manasseh Daniel Jatau shi ya tabbatar da haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.