Bayan Shafe Makonni 2, Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Dawo Najeriya
- Jirgin da ya kai shugaban Najeriya Birtaniya domin yin hutun makonni biyu ya dawo da shi da yamman nan
- A ranar Asabar fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Bola Ahmed Tinubu ya iso birnin tarayya watau Abuja
- Hadimin shugaba Bola Tinubu ya nuna bidiyon dawowarsa a shafinsa, lokacin hutun da ya dauka ya kare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Mai girma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe kwanaki ya na hutu a ketare.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin shugaban Najeriyan ya iso ne a yammacin Asabar, sai ba a kai ga ganinsa ba.
Shugaba Bola Tinubu ya sauka a Abuja
Mai taimakawa Bola Ahmed Tinubu a kafofin sadarwa na zamani, Olusegun Dada ya tabbatar da hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusegun Dada ya yi magana ya na mai nuna jirgin fadar shugaban Najeriya ya sauka.
‘Barka da zuwa shugaban kasa’
- Olusegun Dada
Yaushe Tinubu ya iso Najeriya?
An tabbatar da wannan zance da kimanin karfe 7:20 na yammacin yau 19 ga watan Oktoba dandalin sada zumuntan.
Wasu bidiyo biyu da aka wallafa sun nuna jirgin shugaban kasar ya na sauka a filin tashi da saukar jiragen sama a Abuja.
A wani gajeren bidiyon kuma an ga mutane su na fareti cikin duhu domin tarbar shugaban kasa kamar dai yadda aka saba.
Hutun Tinubu a Turai ya kare
Rahoton The Cable ya ce shugaba Bola Tinubu ya dawo gida ne bayan ya dauki makonni biyu ya na hutawa a Birtaniya.
Idan za a tuna, Tinubu ya bar Najeriya ne a farkon watan Oktoban nan, ya yi kwanaki 17 tsakanin kasashen Ingila da Faransa.
Ministocin Tinubu sun sha kenan?
Ana sa rai zuwa ranar Litinin a ga shugaban kasan a ofis, kuma watakila zai iya jagorantar zaman majalisar zartarwa (FEC).
An dai ta yada cewa Tinubu zai iya amfani da damar wannan tafiya da ya yi domin yin canji a majalisar ministocin tarayya.
Masoyan APC da ke sukar Tinubu
An kawo rahoton 'yan APC da suka koma sukar gwamnatin Bola Tinubu. Alal Joe Igbokwe ya na cikin masoyan APC a baya.
Sukar gwamnatin Bola Tinubu ne ya jawo Muhammad Ali Ndume ya rasa matsayinsa a majalisa kuma har yau bai daina.
Asali: Legit.ng