'Ku Cigaba da 'Mining': Shehin Malami Ya Karawa Yan Baiwa Himma, Akwai Yiwuwar Ya Fara
- Sheikh Salihu Abubakar Zaria ya karawa yan baiwa ƙarfin guiwa game da cigaba da 'mining' da suke yi inda ya yi musu addu'a
- Shehin Malamin ya ce 'mining' halal ne inda ya bukaci yan baiwa su cigaba da yi su samu alheri kan abin da suke yi
- Malamin ya ce tun da yake bai taba yin 'mining' ba a rayuwarsa amma idan yana da rabon samu wataran za a gani yana yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Malamin Musulunci, Sheikh Abubakar Salihu ya sake magana kan 'mining' da ake yi.
Shehin Malamin ya tabbatar da maganarsa inda ya halatta yin 'mining' kamar yadda ya fada a baya.
Malam ya ce babu matsala a yin 'mining'
Sheikh Salihu Zaria ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar DCL Hausa da ta wallafa bidiyon a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehin Malamin ya ce babu wata matsala game da 'mining' saboda aiki mutum ya yi aka biya shi saboda ba aikin banza ya yi ba.
Malamin ya ce idan Allah ya sa yana da rabo shi ma wataran zai yi 'mining' amma a yanzu bai taba yi ba.
"Mining halal ne, ina kan baka ta 'mining' babu matsala, yan baiwa su yi ta 'mining' Allah ya sanya albarka."
"Tun da Allah ya halicce ni ban taba yin 'mining' ba amma idan Allah ya sa ina da rabo za ka gani ina yi."
- Sheikh Salihu Zaria
Sheikh Salihu Zaria ya karawa yan 'mining' ƙarfi
Sheikh Salihu Zaria ya ce aikin kwadago masu 'mining' suke yi aka biya su inda ya ce halal suke ci.
Malamin ya ce a duk lokacin matasa ke son karatu babu hali kuma babu sana'a komai zai ya faruwa.
Shehi ya ba da misali yadda matasa suka yi barna a lokacin zanga-zanga saboda halin da ake ciki na rashin aikin yi da tsadar rayuwa.
Sheikh Salihu ya magantu kan tikitin Muslim/Muslim
Kun ji cewa Malam Salihu Abubakar Zaria ya bayyana cewa ko kadan bai yi nadamar zaben Bola Tinubu a tsarin Musulmi da Musulmi ba.
Sheikh Salihu ya ce ko kadan ba tsarin Musulmi da Musulmi ba ne ya kawo damuwar da ake ciki inda ya ce daga Allah ne.
Asali: Legit.ng