Malaman Musulunci 5 da Za Su Iya Goyon Bayan Tinubu idan Ya Nemi Tazarce a 2027

Malaman Musulunci 5 da Za Su Iya Goyon Bayan Tinubu idan Ya Nemi Tazarce a 2027

Abuja - 2027 za a sake yin zaben shugaban kasa kuma Bola Ahmed Tinubu bai taba nuna maganar tazarce na gabansa ba a yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

A shekarar 2027, ana kyautata zaton Bola Tinubu zai sake neman mulkin Najeriya kamar yadda ya tsaya takara a APC a zaben 2023.

Abin da mu ka yi a wannan rahoto shi ne tattaro wasu malaman addinin da mu ke tunanin za su goyi bayan APC a babban zabe na 2027.

Bola Tinubu
Watakila malaman musuluncin su taya Bola Tinubu yakin zabe a 2027 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Malaman da za su iya goyon bayan Tinubu a 2027

1. Muhammad Bn Uthman

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da aka yi zaben 2027, Sheikh Muhammad Bn Uthman ya taimakawa APC saboda ganin yadda aka dauko musulmi da musulmi.

Kara karanta wannan

"Na cancanta," Sanatan APC ya bayyana shirinsa na neman zama shugaban ƙasa a 2027

Babu mamaki a zabe mai zuwa ya goyi bayan Bola Tinubu wanda ya nada sa a matsayin daya daga cikin kwamishinoin hukumar NAHCON.

2. Sani Yahaya Jingir

Daily Trust ta rahoto yadda Sani Yahaya Jingir ya taka rawar gani wajen tallata Bola Tinubu da Kashim Shettima ganin cewa su musulmai ne.

La’akari da yadda yake kare gwamnatin APC a halin yanzu, Legit ta na tunanin ko gobe aka fito takara zai fadawa mabiyansa su bi Tinubu.

3. Abdullahi Saleh Fakistan

Sheikh Abdullahi Saleh Fakistan ya na cikin malaman addinin da ke da alaka da gwamnatin APC a sanadiyyar Dr. Abdullahi Ganduje.

Malamin ya taya jam’iyyar APC rike mulkin Kano a 2019 kuma kwanaki shugaba Bola Tinubu ya nada shi ya zama shugaban hukumar hajji.

4. Abubakar Salihu Zaria

Wani malami daga bangaren Izalar Jos da ake ganin zai iya ba APC gudumuwa idan ta sake neman takara shi ne Abubakar Salihu Zaria.

Kara karanta wannan

"Kuna da damar taimakon ƴan Najeriya," Jigon APC ya dura kan Kwankwaso da Atiku

Alkali Abubakar Zaria ya tallata Bola Tinubu a 2023 kuma ya fada da bakinsa cewa duk da halin kuncin da ake ciki a yau, bai yi nadama ba.

5. Isa Ali Ibrahim Pantami

Daga baya an ji labarin kokarin da Sheikh Isa Ali Pantami ya yi wajen ganin jam'iyyar APC ta rike mulki bayan Muhammadu Buhari ya sauka.

A lokacin ya na minista a gwamnatin tarayya, malamin addinin ya yi wa APC kamfe, kuma an ga shi ya na farin ciki da Bola Tinubu ya yi galaba.

Malamin musulunci ya tabo gwamnan Bauchi

Ana da labarin yadda babban malamin nan dris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya zargi gwamna Bala Mohammed da karbe filin sallarsu.

Sheikh Dutsen Tanshi ya maidawa gwamnan martani, ya tuno abin da ya faru a Kano da Abdullahi Ganduje ya raba filaye a masallacin idi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng