An Barke da Murna da Kamfanin NNPCL da Chevron Suka Sake Gano Wata Rijiyar Mai
- Yayin da ake cikin wani hali na tsadar mai a Najeriya, kamfanonin NNPCL da Chevron sun sake samun nasara
- Kamfanonin sun yi nasarar hakar wata rijiyar mai da aka samu alheri a Yammacin Neja Delta da ke Kudancin kasar
- Babban manajan Chevron, Olusoga Oduselu ya tabbatar da haka a yau Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bayelsa - Kamfanin NNPCL da Chevron Nigeria Limited sun yi nasarar samun wata rijiyar mai a Najeriya.
Kamfanonin biyu sun samu nasarar hakan rijiyar a yankin Yammacin Neja Delta masu arzikin man fetur.
NNPCL ta samo wata rijiyar mai a Najeriya
The Guardian ta ce hakan zai kara inganta harkokin makamashi a Najeriya da farfaɗo da tattalin arziki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban manajan kamfanin Chevron, Olusoga Oduselu shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024.
Oduselu ya ce sun samu nasarar da hadin guiwar kamfanin NNPCL kan aikin hakar rijiyar man, cewar rahoton Punch.
Ya ce aƙalla sun yi nasarar tonon kafa 8,983 a cikin kasa a tsakiyar watan Satumbar 2024, BusinessDay ta tabbatar a rahotonta.
Rahotanni sun tabbatar da cewa rijiyar da aka haka za ta iya samar da akalla hanga 17,000 na danyen mai.
Karanta wasu labaran NNPCL da harkokin mai
- Shugaban NNPCL Ya Bayyana Ribar da Ake Samu daga Fasa Kwaurin Man Fetur
- Fetur zai Sauka,’ IPMAN Ta yi Bayani bayan Cimma Matsayar Farashi da NNPCL
- Farashin fetur: NNPCL Ya Musanta Cimma Yarjejeniya da IPMAN, Ya Bayyana Yadda Abin Yake
Majalisar Tarayya ta shiga lamarin tsadar mai
Kun ji cewa mai yiwuwa a samu saukin tsadar man fetur da majalisar wakilan tarayya ta sa baki kan ƙarin farashin lita a Najeriya.
A zamanta, majalisar ta buƙaci a gaggauta soke ƙarin farashin da aka yi kwanan nan saboda ya kara jefa mutane cikin wahala.
Tun bayan cire tallafin mai ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ƴan Najeriya suka fara fuskantar tsadar fetur da ba a taba gani ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng