Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda, Sun Kwato Makamai Masu Yawa
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka ƴan ta'adda a jihohin Borno da Yobe da ke yankin Arewa maso Gabas
- Biyu daga cikin ƴan ta'addan da aka kashe a jihar Yobe, an hallaka su ne a wajen wani wurin karɓar haraji a garin Gujba
- Dakarun sojojin kasar sun kuma samu nasarar ƙwato wasu makamai masu tarin yawa a hannun miyagun ƴan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sojojin Najeriya da aka tura domin yaƙi da ta'addanci a jihohin Yobe da Borno sun kashe ƴan ta'adda aƙalla guda huɗu.
Dakarun sojojin sun samu nasarar kashe ƴan ta'addan ne a jihohin Borno da Yobe.
Yadda sojoji suka kashe ƴan ta'addan
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta sanya a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai a hannun ƴan ta'addan masu tayar da ƙayar baya.
Ƴan ta’adda biyu da aka kashe a Yobe na daga cikin waɗanda ke aikin karɓar haraji a yankin Ngazargamu da ke ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe.
Dakarun sojojin sun yi aiki da bayanan sirrin da suka samu ne wanda hakan ya sanya suka farmaki ƴan ta'addan.
Sojoji sun yi galaba kan ƴan ta'adda
"A ƙaramar hukumar Gujba da ke jihar Yobe, bayan samun bayanan sirri, sojoji sun ƙaddamar da farmaki kan ƴan ta'addan Boko Haram da ke aiki a wurin karɓar haraji a yankin Ngazargamu."
"A arangamar da suka yi, sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta’adda biyu tare da ƙwato tarin makamai da suka haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, bindiga ƙirar FN guda ɗaya, alburusai da wayoyin hannu guda uku."
"Hakazalika, a kan hanyar Gamboru zuwa Logomane a jihar Borno, sojoji sun yi wa mayaƙan ISWAP kwanton ɓauna, inda suka kashe ƴan ta’adda biyu. Sojojin sun kuma ƙwato bindigu kirar AK-47 guda biyu da sauran kayayyaki."
Dakarun Sojoji sun sheƙe ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce dakarun sojoji sun ƙara samun galaba a yaƙi da ƴan ta'adda a Arewacin Najeriya.
DHQ ta bayyana cewa sojoji sun samu nasarar aika ƴan ta'adda 96 barzahu, sannan sun cafke wasu 227 da ake zargi da aikata manyan laifuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng