‘Ana Shan Wuya,’ Wani Babba a APC Ya Cire Kunya Ya Koka da Mulkin Tinubu

‘Ana Shan Wuya,’ Wani Babba a APC Ya Cire Kunya Ya Koka da Mulkin Tinubu

  • Jigo a jam'iyyar APC, Joe Igbokwe ya yi kuka kan yadda lamura ke kara rugujewa a karkashin mulkin Bola Ahmed Tinubu
  • Joe Igbokwe ya yi martani kan maganar da bankin duniya ya yi na cewa kudin Najeriya na cikin marasa daraja a Afirka
  • Haka zalika ya yi zargin cewa a yanzu kusan dukkan 'yan siyasa' kansu suka sani, ba gyaran Najeriya suka saka gaba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jigon APC, Joe Igbokwe ya nuna damuwa kan inda Najeriya ta dosa saboda ganin yadda abubuwa ke kara dagulewa.

Mista Joe Igbokwe ya yi ishara da cewa halin da ake ciki a Najeriya na neman cire masa tsammanin samun sauki ko gyara.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Joe Igbokwe
Babban dan APC ya yi kuka kan kunciin rayuwa. Hoto: Joe Igbokwe|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro abin da Joe Igbokwe ya fada ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan APC ya yi tir da rashin darajar Naira

Babba dan APC, Joe Igbokwe ya nuna damuwa kan yadda darajar Naira ta yi baya har ta shiga jerin kudi marar daraja a Afrika.

Karyewar darajar Naira na cikin tsare tsaren da Bola Tinubu ya kawo kuma hakan ya jawo karin wahalar rayuwa ga yan Najeriya.

Joe Igbokwe ya nuna takaici kan lamarin inda yake cewa abin mamaki ne ace kudin Najeriya ya zama ba shi da daraja hatta a Afrika.

Ga abin da ya ce:

"Ya za a ce duk arzikin da Allah ya yi wa Najeriya, kuɗinta ba shi da karaja a nahiyar Afirka?"

Kara karanta wannan

T-Pain da sauran sunaye 4 da aka lakawa Tinubu da dalilan alakanta shi da su

"Ina basirar mu ta tafi?"

- Joe Igbokwe, jigon APC

Kusa a APC ya koka kan matsin rayuwa

Joe Igbokwe ya ce a yanzu shugabannin Najeriya kawai suna magance matsalolin kansu ne ba gyaran ƙasa ba.

A halin da ake ciki, Igbokwe ya ce ya zo makura wajen shiga matsala kuma duk wani kokari ko fata da yake da shi ya ƙare.

Daily Trust ta ruwaito cewa ko a watan Satumba Joe Igbokwe ya koka kan karin kudin wuta, ya bukaci a kawo dauki.

Kalu ya ce APC za ta ci zaɓe a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ko a yau aka ce za a yi zabe a Najeriya yana da tabbacin cewa APC za ta yi nasara.

Sanata Orji Uzor Kalu ya bayyana dabarar da za su yi wajen shawo kan talakawan Najeriya yayin zabe kuma ba za su juwa musu baya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng