Katsina: Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Kashe Jami'in Tsaro

Katsina: Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Kashe Jami'in Tsaro

  • Yan bindiga sun kai hari a jihar Katsina inda suka sace shugaban jam'iyyar APC a yankin karamar hukumar Sabuwa
  • Maharan, yayin harin sun kuma hallaka wasu mutane bayan sace tulin mata da yara a yankin karamar hukumar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai harin ne a yau Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024 a kauyen Dan Auta a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Wasu yan bindiga sun kai hari a jihar Katsina, sun hallaka mutane biyu da jami'in tsaro guda daya.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar a yau Juma'a 18 ga watan Oktoban 2024.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban APC a Katsina
Yan bindiga sun hallaka wasu mutane da kuma sace shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun hallaka jami'in tsaro a Katsina

The Guardian ta ce maharan kuma sun sace shugaban jam'iyyar APC a yankin da aka bayyana da Alhaji Imamu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar cewa daga cikin wadanda aka hallaka akwai jami'in tsaro na hukumar KSCWC da aka kafa a jihar.

Har ila yau, yayin harin kusa da kauyen Dan Auta, an tabbatar da cewa an sace yara da mata fiye da 13.

Yadda yan bindiga suka ci karo da cikas

Bayan kisan da maharan suka yi, sun kuma raunana mutane da dama waɗanda ke karbar kulawa a asibiti.

Yan bindiga sun ci karo da cikas daga yan banga da kuma hukumar tsaro ta KSCWC inda maharan suka yi nasarar fatattakarsu.

An tabbatar cewa jami'in tsaro daya ya rasa ransa a kokarin dakile harin yayin da aka harba wani daban saboda ya yi kokarin guduwa.

Kara karanta wannan

Igbo sun yi nasarar lashe kujeru a zaben kananan hukumomi a Arewacin Najeriya

Ta'addanci: An cafke basarake a jihar Katsina

Kun ji cewa Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta cafke wani basarake da ake zargi da taimakon yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun nuna cewa yan sanda sun kama basaraken ne a yankin jihar Kaduna bayan samun bayanan sirri a kansa.

Haka zalika basaraken ya fadi yan ta'adda da yake da alaka da su da kuma wasu miyagu da suke aikin taimakon yan bindiga tare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.