"Tinubu ba zai Iya ba:" Malamin Addini Ya Tura Shawara kan Tattalin Arziki

"Tinubu ba zai Iya ba:" Malamin Addini Ya Tura Shawara kan Tattalin Arziki

  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta iya komai ba
  • Ya bayyana cewa matsalar tattalin arzikin kasar nan ya fi karfin gwamnatin tarayya, kuma shugaba Tinubu ya san da haka
  • Ya bayar da shawara kan sake fasalta tattalin arzikin yadda ba za a kai ga shiga mawuyacin halin da ya fi yanzu Ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya ce gwamnatin Najeriya ta san ba za ta iya magance matsalar tattalin arziki ba.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da hadimin limamin cocin, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu a ranar Juma'a.

Tinubu
Malamin addini ya ce Tinubu zai gaza Hoto: Bayo Onanuga/Primate Babatunde Elijah Ayodele
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro shugaban cocin ya kara da tunawa yan Najeriya halin da tattalin arziki ke ciki, tare da hasashen abin da zai faru a nan gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limamin coci ya yi hasashe kan tattalin arziki

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa shugaban cocin INRI, 'Primate' Babatunde Ayodele ya ce tattakin arzikin kasar nan zai cigaba da shiga mawuyacin hali.

Ya yi hasashen gwamnatin tarayya za ta cigaba da dorawa jama'a haraji da matse hannu, wanda haka zai kara matse jama'a fiye da yanzu.

Shugaban coci ya shawarci Tinubu

Primage Oyedele ya shawarci Bola Ahmed Tinubu da kar ya takure yan kasar nan har ta kai ga ana tsintar abin da za a ci daga bola.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan maido tallafin man fetur

Ya yi gargadin cewa tattakin arzikin Najeriya zai ruguje matukar ba a sake fasalta shi yadda zai dawo aiki yadda ya dace ba.

" Tinubu zai gyara kasa:" Sanata

A baya mun wallafa cewa Sanata Orji Kalu da ke wakiltar Abia ta Arewa ya bayyana gamsuwa da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu za ta gyara kasar nan.

Ya bayyana haka bisa dalilinsa na cewa shugaban na kokarin sanin halin da jama'a ke ciki, domin da kansa ya ke shiga cikin jama'a da daddare don ganin yadda su ke rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.