DHQ: Dakarun Sojoji Sun Cafke Kasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Hallaka Wasu Kusan 100

DHQ: Dakarun Sojoji Sun Cafke Kasurgumin Ɗan Bindiga, Sun Hallaka Wasu Kusan 100

  • Kamar yadda ta saba mako-mako, hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu a makon jiya
  • DHQ ta ce dakarun rundunar sojoji ta yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 96, sun cafke wani kwamandan ƴan bindiga Usman Maisaje
  • Ta ce sojojin sun kama miyagu 227 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da ceto mutane 157 daga hannun miyagu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta ce dakarun sojoji sun ƙara samun galaba a yaƙi da ƴan ta'adda a Arewacin Najeriya.

DHQ ta bayyana cewa sojoji sun samu nasarar aika ƴan ta'adda 96 barzahu, sannan sun cafke wasu 227 da ake zargi da aikata manyan laifuka.

Kara karanta wannan

NNPP: Jam'iyyar Kwankwaso ta buɗe ƙofa, za a yi wa Tinubu taron dangi a 2027

Sojojin Najeriya.
Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da sojoji suka samu a mako ɗaya a Najeriya Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kama jagoran ƴan ta'adda

Ya ce daga cikin miyagun da sojojin suka cafke har da wani kasurgumin ɗan ta'adda wanda aka fi sani da Usman Maisaje.

Edward Buba ya ce Maisaje na ɗaya daga cikin na hannun daman babban jagoran ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo mai suna Kachalla Boka.

Kakakin DHQ ya ƙara da cewa Usman Maisaje ya fara ba sojoji haɗin kai ta hanyar ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a Arewa.

Nasarorin sojoji a mako guda a Najeriya

"A makon jiya sojoji sun kashe ƴan bindiga 96, sun kama wasu 227, tare da ceto mutane 157 da aka yi garkuwa da su."

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

"Sojoji sun kama wani fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda mai suna Usman Maisaje, makausanci ne ga kasurgumin ɗan bindigar da ake nema, Kachalla Boka," in ji Buba.

Edward Buba ya ci gaba da cewa sojojin sun kuma kwato makamai kala daban-daban guda 71 da alburusai 1,463.

Sojojin sama za su samu ƙarin jiragen yaƙi

A wani rahoton kuma rundunar sojin Najeriya ta sanar da shirin mallakar karin jiragen yaki domin kawar da yan bindiga da sauran yan ta'adda.

Shugaban sojin saman Nigeriya, Hassan Abubakar ne ya bayyana shirin da suke a wani taron sojoji a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262