Peter Obi Ya Caccaki Yadda Tinubu, Shettima Su ka Bar Najeriya da Matsala

Peter Obi Ya Caccaki Yadda Tinubu, Shettima Su ka Bar Najeriya da Matsala

  • Dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi ya bayyana rashin dacewar barin kasar nan ba tare da shugabanninta a fadar gwamnati ba
  • Peter Obi na yin martani ne kan yadda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Bola Tinubu duk suka bar kasar zuwa ketare
  • Ya bayyana cewa Najeriya na fama da tulin matsaloli, kuma akwai rashin dacewa kan yadda shugaba da mataimakinsa su ka fice daga kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya bayyana damuwa a kan yadda kasar nan ke tafiya babu shugabanta ko mataimaki a fadar gwamnati.

Kara karanta wannan

'Yana yawo cikin dare,' Sanata ya tona yadda Tinubu yake zagaya gari a boye

Peter Obi na ganin hakan bai dace ba, ganin yadda kasar nan ke fama da tarin matsaloli kama daga na tattalin arziki zuwa na tsaro.

Tinubu
Peter ObI ya ga rashin dacewar yadda Tinubu da Shettima su ka bar Njaeriya Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi ya yi mamakin yadda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bar kasar alhali shugaba Tinubu bai dawo ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya caccaki karin hutun Bola Tinubu

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Peter Obi ya yi zargin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bar kasar nan da zimmar zai dawo bayan kwanaki 14.

Peter Obi ya ga rashin dacewar tafiyar Shettima taro Sweden, maimakon shugaban kasa , Bola Ahmed Tinubu ya biyawa taron a hanyarsa ta dawowa daga Faransa.

Peter Obi ya ga gazawar gwamnatin Tinubu

Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya ce Najeriya na fama da tarin matsalolin da ke bukatar agajin gaggawa.

Kara karanta wannan

'Alamar matsala tsakanin Tinubu da Shettima,' Hadimin Osinbajo ya fito da bayanai

Ya ce manufofin gwamnatin nan sun jawo wahalar da ta jefa jama'a a cikin rashin walwala, hadi da bukatar gwamnati ta mayar da hankali kan kawo gyara.

Sanata ya ce Tinubu zai magance talauci

A wani labarin mun ruwaito cewa Orji Kalu mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar kasar nan ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na sane da matsalolin da ke damun yan Najeriya.

Orji Kalu ya kara da cewa shugaban ya san da matsalolin da ake ciki ne saboda ya kan yi tattaki da daddare domin ganin yadda jama'a ke rayuwa a babban birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.