An Canza Salo: Gwamnatin Najeriya Ta Fitar da Bayanai kan Yi wa Yan Bindiga Tarko
- Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya gana da gwamnan Kaduna kan shirin yakar yan bindiga
- Muhammadu Badaru Abubakar ya fadi kokarin da suke yi na ganin sun makure yan bindiga a waje daya, a hana su ta'adi
- Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi magana kan rawar da gwamnonin jihohin Arewa za su taka wajen yakar yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Ministan tsaro ya ziyarci jihar Kaduna a kokarin shawo kan matsalolin tsaron Najeriya.
Muhammad Badaru Abubakar ya ce suna ƙoƙarin samun hadin kan kasashen da ke kusa da Najeriya kan tsaron iyakoki.
Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya ce za su hada kai wajen fuskantar matsalar tsaro a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya na shirin haɗaka da kasar Nijar
Ministan tsaro ya bayyana cewa suna tattaunawa da ƙasar Nijar domin shirin yin tarko ga yan bindiga da ke iyakokin kasashen biyu.
Badaru Abubakar ya bayyana cewa yan bindiga na yawan farautar mutane da safarar makamai a kan iyakokin Najeriya da Nijar.
Hadakar za ta taimaka wajen yin tarko da daƙile zirga zirgar yan ta'addan a iyakokin Najeriya da Nijar musamman idan aka matsa musu lamba.
Damuwar Tinubu kan tsaron Najeriya
Badaru Abubakar ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu kullum yana jaddada musu maganar kawo karshen yan bindiga.
A karkashin haka, ministan ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin sun samu cikakkiyar nasara a kan miyagun ƙasar nan.
Uba Sani ya yi magana kan tsaro
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayyana cewa dole su samar da cibiyar haɗaka a tsakaninsu domin kawo karshen matsalolin tsaro a Arewa ta Yamma.
Uba Sani ya jadda cewa za su cigaba da bayar da cikakkiyar gudunmawa ga jami'an tsaron Najeriya domin tabbatar da kawo karshen yan bindiga.
Sojoji za su saye jiragen yaki 50
A wani labarin, Legit ta ruwaito cewa rundunar sojin saman Nigeriya za ta saye sababbin jiragen yaki 50 daga nan zuwa 2026.
Shugaban sojin saman Najeriya, Hassan Abubakar ne ya bayyana haka yayin wani taron manyan sojoji a birnin tarayya Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng