CNG: Masu Motoci Sun Ki Rungumar Gas duk da Yunkurin Gwamnati da Tsadar Fetur

CNG: Masu Motoci Sun Ki Rungumar Gas duk da Yunkurin Gwamnati da Tsadar Fetur

Gwamnatin tarayya na tallata yin amfani da man iskar gas na CNG ga ƴan Najeriya yayin da man fetur ya yi ɗan karan tsada a ƙasar nan.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Man iskar gas na CNG yana da arha wanda hakan ya sanya zama makwafin man fetur domin yin amfani da shi a motoci.

Masu motoci sun ki komawa CNG
Masu motoci na kaffa kaffa da komawa amfani da CNG Hoto: Bloomberg, Contributor
Asali: UGC

Gwamnati na so a rungumi CNG a motoci

Gwamnatin tarayya ta fito da tsarin PCNGi wanda zai mayar da hankali wajen ganin an koma amfani da CNG a ƙasar nan domin samun sauƙi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ƙarƙashin tsarin akwai shirin samar da wuraren da za a riƙa mayar da motoci masu amfani da man fetur komawa yin amfani da CNG.

Kara karanta wannan

Abuja, Kaduna da Wasu Jihohi 7 da Yan Najeriya Za Su Iya Komawa Amfani da CNG

Tsarin zai kuma samar da motoci masu amfani da CNG domin sauƙaƙa kuɗin sufuri a faɗin ƙasar nan.

Tuni gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wasu motoci masu amfani da CNG.

Meyasa mutane ke tsoron CNG?

1. Tsoron fashewa

Mutane da dama sun nuna fargaba kan yiwuwar samun fashewa idan suka koma amfani da CNG maimakon fetur a motocinsu.

2. Tsada

Wasu sun koka da yadda mayar da motocin zuwa masu amfani da CNG ya yi tsada da rashin wuraren da ake mayarwa a inda suke zaune.

3. Ƙarancin wuraren da ake aikin

Akwai ƙarancin wuraren da mutane za su iya zuwa domin mayar da motocinsu su koma masu amfani da CNG.

Hakan ya taka wajen hana wasu da ke da niyyar mayar da motocinsu rungumar tsarin domin a wuraren da suke zaune ba a fara ba tukunna.

Ra'ayin mutane kan komawa motocin CNG

Legit Hausa ta samu jin ta bakin mutane da dama kan ko suna da shirin mayar da motocinsu su koma amfani da CNG domin samun sauƙi wajen kashe kuɗi saboda tsadar fetur.

Kara karanta wannan

CNG: Gwamnati ta bayyana abin da ya jawo wata mota mai amfani da gas ta fashe

Da yawa daga cikinsu sun nuna shakku kan mayar da motocinsu masu amfani da CNG saboda abin da suka kira hatsarin da ke tattare da hakan.

Ibrahim Zulkiful ya bayyana cewa a baya yana da ra'ayin mayar da motarsa ta koma amfani da CNG amma a yanzu ya canza shawara.

"Da gaskiya na yi tunanin na mayar da mota ta mai amfani da CNG domin har na kira an gaya min kuɗin da zan kashe. Amma yanzu gaskiya na canza shawara saboda na lura akwai hatsari a ciki."

- Ibrahim Zulkiful

Aliyu Dauda ya bayyana cewa tun da farko bai yi niyyar mayar da motarsa hakan ba saboda fargabar abin da zai iya faruwa na fashewar gas ɗin.

"Ai gaskiya ba zan iya maida motata mai amfani da CNG ba. Abin nan akwai ban tsoro, idan aka samu matsala abin baya yin kyau."

- Aliyu Dauda

Nawa ake kashewa mota ta koma amfani da CNG?

Kara karanta wannan

Magidanci a Kano ya shiga matsala bayan ya raunata matarsa a wuri mai daraja

Gwamnatin tarayya ta kawo tsarin mayar da motoci zuwa masu amfani da CNG kyauta ga motocin masu sufuri na ƙungiyar NURTW.

Bayanai sun nuna An dai zaɓi wasu daga cikinsu ne domin ɗora su a kan tsarin.

Injiniya Mike wanda yake aiki a NITT Zaria ya bayyana cewa har yanzu gwamnati ba ta a sanya farashin mayar da motocin ba ga masu buƙata.

Sai dai, ya bayyana cewa akwai wurare masu zaman kansu waɗanda suke mayar da motocin zuwa masu amfani da CNG ga masu buƙata.

Ya bayyana cewa a irin waɗannan wuraren farashin yana kai kusan N1.2m.

Gwamnati za ta raba keke masu amfani da CNG

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bude shafin da matasan kasar nan za su iya neman Keke Napep mai amfani da gas din CNG wanda za ta raba nan da dan wani lokaci.

Kara karanta wannan

CNG: Ana jimamin hatsarin Jigawa, mota mai amfani da gas ta fashe a gidan mai

Ma'aikatar ci gaban matasa ta sanar da cewa matasan Najeriya musamman wadanda ke harkar sufuri za su cike fom na neman samun Keke Napep din a shafinta na intanet.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng