Yan Bindiga Sun Bani: Sojoji Za Su Samu Jiragen Yaki 50 domin Zafafa Luguden Wuta
- Rundunar sojin Najeriya ta sanar da shirin mallakar karin jiragen yaki domin kawar da yan bindiga da sauran yan ta'adda
- Shugaban sojin saman Nigeriya, Hassan Abubakar ne ya bayyana shirin da suke a wani taron sojoji a birnin tarayya Abuja
- Hassan Abubakar ya bayyana lokacin da za su samu karin jiragen da ma wasu matakai da suke dauka domin inganta tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta yi bayani kan shirin da take yi na magance matsalolin tsaron kasar nan.
Shugaban sojojin saman Najeriya, Hassan Abubakar ya bayyana cewa suna shirin mallakar karin jiragen yaki.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban sojojin ya yi bayani ne yayin wani taro da manyan sojojin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar Sojoji za ta karo jiragen yaki 50
Shugaban sojin saman Nigeriya, Hassan Abubakar ya bayyana cewa za su karo jiragen yaki 50 domin zafafa luguden wuta kan miyagu.
The Nation ta wallafa cewa Hassan Abubakar ya bayyana cewa ko a cikin wannan shekarar rundunar sojin ta saye jiragen yaki 12.
Sojojin sama za su zafafa luguden wuta
Hafsun sojin saman Nigeriya ya ce za su saye sababbin jiragen yakin ne domin cigaba da kai zafafan hare hare kan miyagu yan bindiga da sauransu.
Ya kuma tabbatar da cewa hakan na cikin kokarin ganin rundunar sojin Najeriya ta cigaba da samun nasara kan yan ta'adda.
Yaushe jiragen yakin za su iso?
A bayanin da ya yi, shugaban sojojin ya bayyana cewa daga watan Disamban 2024 zuwa shekarar 2026 ake tsammanin samun dukkan jiragen.
Ya kuma bayyana cewa wannan kokarin na cikin nasarorin da rundunar sojin ta dade ba ta samu ba tsawon shekaru.
Haka zalika ya karfafi gwiwar kwamandojin sojoji tare da fatan za su karfafi jami'an da ke karkashinsu wajen kara ƙaimi.
An buƙaci canza salon yaki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar farar hula ta bukaci gwamnatin tarayya ta canza salon yaki da yan ta'addan Kudu maso Gabas.
Kungiyar ta bukaci a saki jagoran yan ta'addar IPOB, Nnamdi Kanu domin taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaron yankin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng