Hadarin Tanka: Abba Ya Kafa Tarihi tsakanin Gwamnoni, Ya Raba Miliyoyi a Jigawa

Hadarin Tanka: Abba Ya Kafa Tarihi tsakanin Gwamnoni, Ya Raba Miliyoyi a Jigawa

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kasance gwamna na farko da ya taka kafa a jihar Jigawa domin ba da tallafi da jaje
  • Abba Yusuf ya gana da gwamna Umar Namadi a fadar gwamnatin Jigawa, ya yi jaje ga waɗanda hadarin fetur ya shafa
  • Bayan jajen, gwamnan ya mika kyautar N100m ga jihar Jigawa domin tallafawa iyalan wadanda suka shiga tsautsayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - Abba Kabir Yusuf ya dura jihar Jigawa domin jaje ga wadanda hadarin tankar mai ya ritsa da su.

A ranar Laraba ne ne aka samu mummunan haɗarin tankar mai inda mutane sama da 150 suka rigamu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

Abba Kabir
Abba ya ba da tallafin N100m a Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

Hadimin gwamnan Jigawa, Garba Muhammad ya bayyana kyautar miliyoyin da Abba Kabir Yusuf ya yi a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya yi wa Jigawa jaje

Abba Kabir Yusuf ya sauka jihar Jigawa da tawaga mai karfi domin yin jaje kan hadarin tankar mai.

Abba Kabir Yusuf ya ba iyalan wadanda suka rasu hakuri yayin da ya yi addu'ar Allah ya ba waɗanda suke kwance a asibiti lafiya.

Abba ya yi kyautar N100m a Jigawa

Bayan sakon jaje da ya mika ga al'ummar jihar, Abba Kabir Yusuf ya mika kyautar kuɗi har Naira miliyan 100.

Ana sa ran za a yi amfani da kuɗin ne wajen tallafawa iyalan wadanda suka rasu da wadanda suke kwance a asibitoci.

Gwamnan Jigawa, Namadi ya godewa Abba

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar A. Namadi ya yi godiya ga Abba Kabir Yusuf bisa zuwa har Jigawa domin yin jaje bayan kira ta waya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta yi bincike kan mutuwar mutane sama da 100 a Jigawa

Gwamna Namadi ya bayyana cewa hakan ya nuna irin kyakkyawar alaka da ke tsakanin jihohin Kano da Jigawa.

Za a binciki dalilin hadarin Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin gaggawa domin bincike kan hadarin tankar mai a Jigawa.

Ministan harkokin man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ne ya fitar da sanarwar ya ce dole a gano dalilin domin daukar mataki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng