Halin Kunci: Gwamna a Arewa Ya Kafa Kwamitin Kayyade Farashin Kaya

Halin Kunci: Gwamna a Arewa Ya Kafa Kwamitin Kayyade Farashin Kaya

  • Yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, gwamnatin jihar Niger ta dauki mataki domin saukakawa
  • Gwamnatin jihar ta kafa kwamiti mai mambobi bakwai domin kayyade farashin kayan abinci da na masarufi a Niger
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman a yau Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Niger - Gwamnatin jihar Niger ta lalubo hanyar dakile hauhawan farashin kaya a jihar.

Gwamna Umaru Bago ya kafa kwamiti na musamman domin kayyade farashin kayan masarufi.

Gwamna ya kafa kwamiti domin dakile haihawan farashin kaya
Gwamna Umar Bago ya kafa kwamiti na kayyade farashin kaya a Niger. Hoto: Umaru Bago.
Asali: Facebook

Gwamna Bago ya kafa kwamitin kayyade farashi

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman shi ya bayyana haka a yau Alhamis 17 ga watan Oktoban 2024, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Usman ya ce an kafa kwamitin ne mai mutum bakwai domin kula da farashin kaya a jihar.

Ya ce gwamnatin jihar ta himmatu wurin tabbatar da daidaita farashi duba da halin da ake ciki na tsadar rayuwa.

Ayyukan da kwamitin gwamna zai yi a Niger

Har ila yau, sakataren gwamnatin ya ce kwamitin zai yi duba kan kayyade farashin kaya da kuma dakile yawan boye kayan abinci da ake yi.

Ya ce kwamitin zai tabbatar da daukar mataki musamman idan an cafke wani da saba doka kan lamarin.

"Kwamitin zai yi aiki tare da sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki da yan kasuwa domin samun gudanar da ayyukan da aka daura masa cikin sauki."

- Abubakar Usman

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake cikin halin kunci da tsadar rayuwa tun bayan cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

An kaure tsakanin gwamnati da NLC

Kun ji cewa an samu musayar yawu tsakanin gwamnatin jihar Neja da kungiyar 'yan kwadago kan bukatun da malamai suka gabatarwa gwamnatin.

Kungiyar malaman jihar ta TUC ta lissafa wasu bukatu na malaman firamare da sakandare da har yanzu gwamnatin Neja ba ta cika su ba.

Sai dai gwamnatin jihar ta bakin Dakta Mustapha Ibrahim ta nuna muhimmancin bukatun malaman bai kai yadda TUC ke rurutawa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.