Abuja, Kaduna da Wasu Jihohi 7 da Yan Najeriya Za Su Iya Komawa Amfani da CNG
Gwamnatin tarayya ta buɗe tashoshin canza ababen hawa daga amfani da man fetur zuwa iskar gas watau CNG a jihohi takwas a Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Hakan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka domin rage yawan amfani da mai wanda yake ƙara tsada lokaci bayan lokaci.
A wata sanarwa da shirin PCNGi ya wallafa a shafinsa na X, ya ce gwamnati ta faɗaɗa aikin maida ababen hawa amfani da CNG zuwa jihohi takwas da Abuja.
Sai dai a cewar sanarwar, daga nan zuwa karshen 2024 za a faɗaɗa shirin zuwa wasu jihohi tara a ƙasar nan.
Bola Ahmed Tinubu ya bullo da shirin maida ababen hawa su koma amfani da gas ne domin rage tasirin hauhawar farashin man fetur da rage tsadar sufuri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro muku jerin jihohin da aka fara aikin sa CNG a ababen hawa da wuraren da aka ware domin wannan aiki.
1. Jihar Legas
Legas na ɗaya daga cikin jihohin da aka fara wannan aiki na sanya CNG a motoci kyauta, gwamnati ta samar da tashohin wannan aiki guda shida.
Tribune Nigeria ta ruwaito cewa duk motar da ta koma amfani da CNG za ta sayi gas SMC kan farashin N230, wanda hakan zai rage amfani da fetur.
Tashohin da aka ware domin sa wa motoci CNG kyauta a Legas sune Femadec, Portland, Mezovest, Dana Motors, MBH Power da kuma Autogig.
2. Jihar Kaduna
A Arewa maso Yamma, Kaduna na ɗaya daga cikin jihohin da aka fara sanya CNG a Najeriya, gwamnati ta buɗe tashoshi uku.
Tashohin CNG a Kaduna sun haɗa da Rolling Energy da ke lamba 16715 a garin Kakau da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja.
Sai kuma tashar da aka buɗe a titin Michidi a Kakuri cikin garin Kaduna da kuma titin zuwa Basawa a Palladan Zaria.
3. Babban birnin tarayya Abuja
A birnin tarayya kuma akwai wurare shida da aka ware wanda suka haɗa da NITT da ke titin Asuquo Okon, ABG Dawaki a babban titin Kubwa da Portland a Obafemi Awolowo Way.
Sauran wuraren da ake maida motoci na CNG a Abuja su ne Bovas a Wuse 5, Nicpo da ke Sabon Lugbe kan titin jirgin sama da kuma gidan mai na C&L Smart Energy Solutions Ltd.
Sauran jihohin da aka fara maida motoci na CNG su ne:
4. Jihar Oyo
5. Jihar Ogun
6. Jihar Edo
7. Jihar Delta
8. Jihar Kogi
9. Jihar Nasarawa.
Dailin fashewar motar CNG a Edo
A wani rahoton kuma gwamnati ta yi martani yayin da wani bidiyo da ya bazu a intanet ya nuna lokacin da wata mota mai amfani da CNG ta fashe a Edo
A cikin wata sanarwa, hukumar kula da shirin shugaban kasa na PCNGi ta bayyana fashewar motar a matsayin "abin takaici"
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng