Rashin Tsaro: Dattawan Arewa Sun Yabi Tinubu, Sun Fadi Kokarin da Yake Yi

Rashin Tsaro: Dattawan Arewa Sun Yabi Tinubu, Sun Fadi Kokarin da Yake Yi

  • Ƙungiyar dattawan Arewa ta NEPG ta yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya a yankin
  • Ƙungiyar NEPG ta bayyana cewa ƙoƙarin da Tinubu yake yi wajen magance matsalar rashin tsaro a yankin Arewa, abin a yaba ne
  • Ta buƙaci gwamnonin jihohin Arewa da su haɗa kai da gwamnatin tarayya domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja -Ƙungiyar dattawan Arewa ta Northern Elders Progressives Group (NEPG), ta yabawa ƙoƙarin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan yaƙi da rashin tsaro a yankin Arewa.

Ƙungiyar ta yabawa shugaban ƙasan kan yadda ya maida hankali wajen kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya bayyana yadda Tinubu ya hana shi barin Najeriya

Tinubu ya samu yabo
Kungiyar dattawan Arewa ta yabawa Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Dattawan Arewa sun yabi Tinubu

Shugaban ƙungiyar NEPG reshen Arewa maso Yamma, Alhaji Mustapha Aliyu Dutsinma, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar ya yaba da sabuwar dabarar da Tinubu ya ɓullo da ita wajen tunkarar matsalar rashin tsaro, wacce aka yi wa laƙabi da “Fansan Yamma,", rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

A cewar ƙungiyar yadda Shugaba Tinubu ya maida hankali wajen magance matsalar rashin tsaro, musamman matakin da ya dauka na yin amfani da karfin soji wajen murkushe ƴan bindiga na haifar da ɗa mai ido.

"Mun gamsu cike da farin ciki cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Tinubu a shirye take ta tunkari matsalar rashin tsaro ta hanyar kawar da ƴan bindiga ba tare da nuna musu sassauci ba."

Kara karanta wannan

Fashewar tanka a Jigawa: Uwargidan Tinubu ta yi ta'aziyya mai ratsa zuciya

- Alhaji Mustapha Aliyu Dutsinma

Ƙungiyar dattawan ta buƙaci gwamnonin Arewa musamman na yankin Arewa maso yamma da su hada kai da gwamnatin tarayya domin samun nasara mai ɗorewa a yaƙin da ake yi da ƴan bindiga.

Gwamna Bala ya soki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya sake sukar tsare-tsaren shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba su haifar da komai ba sai matsi da yunwa.

Gwamnan Bala ya ce ya kamata shugaban ƙasa ya sake nazari kan waɗannan tsare-tsaren domin babu wani gyara da suka kawo a rayuwar ƴan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng