‘Ku Ƙaura,’ Gwamnati Ta Gargaɗi Jihohi kan Mummunar Ambaliya

‘Ku Ƙaura,’ Gwamnati Ta Gargaɗi Jihohi kan Mummunar Ambaliya

  • Gwamnatin tarayya ta fitar da sabon gargadi kan mummunar ambaliyar ruwa da ake hasashen za ta afku a wasu jihohin ƙasar
  • Hukumar NIHSA ce ta fitar da gargaɗin biyo bayan yawan ruwan saman da ake samu a yankunan da suke kusa da kogi
  • Daraktan hukumar NIHSA, Umar Muhammad ya buƙaci waɗanda suke kusa da ruwa da su gaggauta kaura domin kubuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar NIHSA ta yi gargadi ga yan Najeriya da suke jihohin da ke kusa da kogin Niger da Benue.

Daraktan NIHSA, Umar Muhammad ya ce kogin ya zo wani mataki mai hadarin gaske da za a iya samun barna sosai idan ambaliya ta barke.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi yadda za ta raba yan Najeriya miliyan 100 da talauci

Ambaliya
An yi hasashen ambaliyar ruwa a wasu jihohi. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a ranar Alhamis, 17 ga watan Oktoba Umar Muhammad ya fitar da sanarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gargaɗi kan ambaliyar ruwa a jihohi

Hukumar NIHSA ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar samun mummunar ambaliyar ruwa a jihohin da suke da kusanci da kogin Niger da Benue.

NIHSA ta ce daga ranar 9 zuwa 15 ga watan Oktoba an samu yawaitar ruwa a yankin kogin wanda hakan alama ce ta ambaliya.

Jihohin da ake fargabar ambaliyar ruwa

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa cikin wuraren da ake fargabar ambaliyar ruwan akwai yankin Ibbi na jihar Taraba.

Haka zalika hukumar ta ce akwai Lokoja a Kogi da yankunan Kainji da Jebba a Niger da wasu yankunan jihar Benue.

NIHSA ta bukaci a kaura daga gidaje

Hukumar NIHSA ta bukaci dukkan waɗanda suke kusa da wuraren da ake hasashen ambaliyar su kaura a gidajen su domin kaucewa shiga matsala.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta yi bincike kan mutuwar mutane sama da 100 a Jigawa

Daraktan hukumar, Umar Muhammad ya buƙaci a dauki matakin da zai kawo karshen matsalar ambaliyar ruwa da ke faruwa a Najeriya duk shekara.

Za a yi bincike kan hadarin Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi umarni a yi bincike domin gano abin da ya jawo mummunan hadarin tankar mai a Jigawa.

Mummunan hadarin ya faru ne cikin dare inda mutane sama da 150 suka rigamu gidan gaskiya, sama da 100 kuma na kwance rai a hannun Allah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng