Gwamnati Za Ta Dauki Mataki bayan Gano Masu Ɗaukar Makamai, Su Aikawa Ƴan ta'adda

Gwamnati Za Ta Dauki Mataki bayan Gano Masu Ɗaukar Makamai, Su Aikawa Ƴan ta'adda

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana takaicin yadda wasu baragurbin jami'anta da mika makaman gwamnati ga bata-gari
  • Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya tabbatar da haka a ranar Alhamis dinnan
  • Nuhu Ribadu ya ja kunnen irin wadannan gurbatattun jami'an gwamnati da cewa su kuka da kansu idan aka kama su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya zargi cewa mafi yawan makaman da ke yawo a hannun bata-garin mutane a kasar nan mallakin gwamnati ne.

Ribadu ya bayyana haka ne yayin atisayen lalata makamai da Cibiyar Kula da Kananan Makamai ta Kasa (NCCSALW), da ta yi a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi yadda za ta raba yan Najeriya miliyan 100 da talauci

Nuhu Ribadu
Gwamnati ta zargi wasu jami'anta da ba yan bindiga makaman gwamnati Hoto: Nuhu Ribadu
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa Nuhu Ribadu ya bayyana cewa an san wadanda su ke mikawa yan bindigar makaman da su ke mallakin gwamnatin kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta fadi masu ba yan bindiga makamai

Jaridar The Nation ta tattaro cewa mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya zargi bara gurbin jami'an tsaronta da ba yan bindiga makamai.

Ya ce gwamnatin tarayya ta na sane da wadanda ke kwasar makaman da aka sayo domin yaki da ta'addanci a fadin kasar nan.

Gwamnati ta gargadi masu ba yan ta'adda makamai

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta yi maganin bara-gurbin jami'anta da ke ba yan ta'adda makaman da aka samar domin wanzar da zaman lafiya.

Mashawarcin shugaba Tinubu kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gwamnati za ta tabbatar da tsaron iyakoki da fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Daidaiton jinsi: Tinubu ya bayyana babban kudurin gwamnatinsa kan matan Najeriya

An kama masu safarar makamai ga yan ta'adda

A wani labarin kun ji cewa rundunar yan sandan kasar nan ta cafke wasu mutane biyu da makaman da ake zargin za su yi safararsu ga yan bindiga a Kaduna.

Tuni wadanda ake zargi, Abdulaziz Habibu da Nuhu Thomas, mazauna Dogon Dawa ne da ke a Birnin Gwari su ka amsa laifin da ake tuhumarsu da shi na safarar makamai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.