Magidanci a Kano Ya Shiga Matsala Bayan Ya Raunata Matarsa a Wuri Mai Daraja

Magidanci a Kano Ya Shiga Matsala Bayan Ya Raunata Matarsa a Wuri Mai Daraja

  • Jami'an ƴan sanda sun cafke wani magidanci, Umar Inusa bisa zargin dukan matarsa a wurin da bai kamata ba a jihar Kano
  • Ƴan sandan sun gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun Musulunci kan tuhumar amfani da karfin tuwo da raunata matarsa
  • Alkalin kotun ya ba da belin Umar saboda har yanzu akwai igiyar aure a tsakaninsu, ya ɗaga zaman zuwa watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda ta sakaya wani magidanci a bayan kanta bisa zargin lakaɗawa matarsa na jaki.

Ƴan sandan sun kuma gurfanar da mutumin mai suna, Umar Inusa gaban kuliya bisa tuhumar ya raunata matarsa a wuri mai daraja a wurin mata watau ƙirji.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago sun cimma matsaya kan farashin kayan abinci

Kotun shari'a.
Wani magidanci ya shiga bayan kanta sakamakon dukan matarsa a Kano Hoto: Shari'a Court
Asali: Getty Images

Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, magidanci ya aikata wannan ɗanyen aiki ne bayan wata ƴar sa-in-sa ta shiga tsakaninsu a tsakar gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Abin da ya haɗa ma'auratan faɗa

Bayanai sun nuna cewa saɓani ya shiga tsakanin ma'auratan ne a lokacin da wanda ake zargin ya tura ƴaƴansa mata zuwa gidan amaryarsa su ci abinci.

To sai dai ɓacin ran da mahaifiyarsu ta nuna kan hakan shi ne ya harzuƙa magidancin ya hau ta da duka.

Ƴan sanda sun tuhumi magidancin da yin amfani da ƙarfin tuwo a kan matarsa, lamarin da ya musanta a gaban alkalin kotun shari'ar Musulunci.

Wane mataki alkali ya ɗauka?

Sai dai bayan sauraron kowane ɓangare, alkalin kotun Mai shari'a Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini ya ba da belin wanda ake zargin.

Alkalin ya amince da buƙatar belin magidancin ne saboda duk da abin da ya faru, har yanzu shi ne mijin matar da aka yi wa rauni a albarkatun ƙirji.

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

Daga nan sai ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba, 2024 domin gabatar da shaidu.

Ango ya kashe amarya a Legas

A wani labarin kuma ana zargin wani matashi da bai jima da aure ba, Motunrayo Olaniyi da cakawa amaryarsa wuƙa har lahira a jihar Legas.

Kakakin ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma'a a yankin Okorodu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262