Gwamna a Arewa Ya Juyawa Tinubu Baya, Ya Ce Manufofinsa Ne Suka Kawo Yunwa
- Gwamna Bala Muhammed ya kara caccakar salon mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da manufofinsa
- Sanata Bala ya ce manufofin shugaban ƙasa ba su haifar da komai ba sai yunwa da wahalar rayuwa a Najeriya
- Ya buƙaci gwamnatin tarayya ta sake tunani domin ƴan Najeriya na cikin fatara da yunwar da ba za ta misaltu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya sake sukar tsare-tsaren shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba su haifar da komai ba sai matsi da yunwa.
Gwamnan Bala ya ce ya kamata shugaban ƙasa ya sake nazari kan waɗannan tsare-tsaren domin babu wani gyara da suka kawo a rayuwar ƴan Najeriya.
Sanata Bala ya faɗi haka ne a wurin kaddamar da shirin kawo ci gaba a Najeriya wanda aka yi a Abuja yau Alhamis, kamar yada Vanguard ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bala Mohammed ya ba Tinubu shawara
Bala Mohammed ya yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu ta guji matakai masu tsauri, inda ya jaddada bukatar kawo sauyi cikin gaggawa saboda wahala ta yi tsanani.
Gwamnan ya bayyana irin halin da talakawan Najeriya ke ciki, inda ya yi gargadin cewa yunwa da matsin tattalin arziki sun jefa mutane cikin baƙar wahala.
Ya ce hatta gwamnoni ba su tsira ba saboda a yadda mutane su ka zo wuya, za su iya farmakar duk wani mai riƙe muƙami.
Manufofin Tinubu ba su aiki
A rahoton Daily Post, Gwamna Bala ya ce:
"A farko mutane sun goyi bayan manufofin shugaban kasa amma a yanzu kuwa ya kamata a sake duba waɗannan manufofi saboda yadda suka kawo matsin rayuwa.
"Mutane na cikin yunwa da wahala kuma waɗannan tsare-tsaren da ake ta ɓaɓatu kansu ba su amfani ƴan Najeriya da komai ba sai matsi."
Gwamna Bala Mohammed na PDP ya ƙara da cewa ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen taimakawa mutane domin su fita daga halin da suke ciki.
Gwamna ya fara gyaran fadar sarakuna
A wani labarin kuma gwamnatin Bauchi na ci gaba da inganta fadojoji sarakuna, hakimai da masu gundumomin jihar domin daga darajar masarautu
A wannan karon, Gwamna Bala Mohammed ya ba da umarnin a gyara fadoji masu gunduma 11 na karamar hukumar Dass a jihar.
Asali: Legit.ng