Yadda Tsohon Sanata Ya Rasu Jim Kadan bayan Kammala Addu'o'i a Gadon Asibiti

Yadda Tsohon Sanata Ya Rasu Jim Kadan bayan Kammala Addu'o'i a Gadon Asibiti

  • Yayin da ake zaman makoki bayan rasuwar Sanata Jonathan Zwingina a Najeriya, tsohon Ministan tarayya ya nuna alhini
  • Jerry Gana ya bayyana kyawawan halayen marigayin inda ya ce ya ba da gudunmawa sosai a rayuwar al'umma
  • Dan marigayin mai suna Kabrh Zwingina ya bayyana yadda mahaifinsa ya bar duniya bayan yin addu'o'i a gadon asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babban dan Sanata Jonathan Zwingina ya yi magana kan rasuwar mahaifinsa a farkon watan Oktoba.

Kabrh Zwingina ya tuno yadda mahaifin nasu ya bar duniya jim kadan bayan kammala addu'o'i na musamman.

An ba da labarin yadda tsohon sanata ya rasu a Najeriya
Dan marigayi tsohon sanata ya fadi yadda mahaifinsa ya cika cikin salama. Hoto: Jonathan Zwingina.
Asali: Facebook

Yadda tsohon sanata ya cika cikin salama

Dan marigayin ya bayyana haka ne yayin da yan uwa da abokan arziki ke bankwana da gawar Sanatan a Abuja, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

'Kun kauce', Malamin Izalah ya soki wasu malaman sunnah da suka koma neman mabiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabrh ya ce mahaifin nasa ya yi bankwana da duniya cikin salama bayan gudanar da addu'o'i a asibiti.

"Ina son yin magana game da lokutan mahaifina na karshe a duniya, na kira Rabaran Tom na ce ina so mu hadu a asibiti."
"Mun hadu a asibiti sai muka fuskanci akwai matsala kan rashin lafiyar, sai Rabaran ya yi mana addu'a na neman yafiya."
"Kammala addu'ar ke da wuya bai wuce dakikai 20 ba kawai sai mahaifinmu ya ce ga garinku nan."

- Kabrh Zwingina

Tsohon Minista ya yi jimamin mutuwar Sanata Zwingina

Tsohon Ministan yada labarai, Jerry Gana ya yabawa da yadda marigayin ya gudanar da rayuwarsa, cewar Daily Post.

"Tabbas rashin Zwingina abin takaici ne, ina tuna lokacin da muka taya shi murnar cika shekaru 70 a duniya."
"Na yi magana a wannan rana a madadin yan uwa da abokan arziki da rashin sanin cewa Zwingina zai bar mu ba da dadewa ba."

Kara karanta wannan

"Allah ji ƙansu," Gwamnan Abba ya yi maganar mutuwar sama da mutum 100 a Jigawa

Jerry Gana

Tsohon sanatan Adamawa ya rasu

Kun ji cewa Allah ya yi wa tsohon sanatan Adamawa ta kudu, Jonathan Silas Zwingina rasuwa yana da shekara 70 a duniya.

Marigayin ya kasance darakta janar na kwamitin yakin neman zaben marigayi MKO Abiola a lokacin zaɓen 1993.

Sanata Jonathan Silas Zwingina babban 'dan siyasa ne kuma yana cikin waɗanda suka kafa PDP a shekarar 1998.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.