"Turakun Wuta za Su Cigaba da Lalacewa:" Ana Magance Matsalar Lantarki

"Turakun Wuta za Su Cigaba da Lalacewa:" Ana Magance Matsalar Lantarki

  • Gwamnatin tarayya ta koka kan tabarbarewar da bangaren wutar lantarki ya yi a fadin kasar, tare da bayyana cewa za a duba lamarin
  • Ministan makamashi na kasar nan, Adebayo Adelabu ne ya bayyana cewa yanzu haka gwamnatin Bola Tinubu ta fara daukar mataki
  • Ya bayyana cewa za a samar da tashoshin wutar lantarki a shiyyoyin kasar nan domin su rika bayar da wuta ga yankunan da su ke

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa dole a cigaba da samun matsalar wutar lantarki a fadin kasar nan, saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

Dillalai sun fadi sakamakon da tattaunawa da matatar Dangote za ta haifar

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka a lokacin da ya kaddamar da kamfanin mitar lantarki a Lekki, Legas.

Lantarki
Gwamnati na shirin gyara matsalar lantarki a Njaeriya Hoto: Transmission Company of Nigeria
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ministan makamashin ya ce amma akwai hanyar da za a bi wajen magance matsalar yawaitar lalacewar turakun lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano hanyar magance matsalar lantarki

Jaridar The Guardian ta tattaro cewa Ministan makamashi na kasar ya ce akwai hanyar da gwamnati za ta bi wajen dakatar da yawan samun matsalar da lantarki ke yi.

Ministan ya ce akwai bukatar sanya manyan tashoshin samar da wutar lantarki a dukkanin shiyyoyin kasar nan da za su rika aiki domin samar da wuta.

Gwamnatin Tinubu na shirin magance matsalar lantarki

Gwamnatin tarayya ta ce ta yi tsayin daka wajen kokarinta na magance matsalar da bangaren wutar lantarki ke fuskanta biyo bayan lalacewar kayan aiki.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi yadda za ta raba yan Najeriya miliyan 100 da talauci

Ministan makamashin kasar nan ya ce tun da gwamnati ta yi nasarar tabbatar da dokar wutar lantarki na shekarar 2023, za a gyara matsalar da sashen ke fuskanta.

Ministan Tinubu ya ce lantarki ya wadata

A baya mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yan kasar nan sun samu wadatar wutar lantarki kamar yadda gwamnatin Bola Tinubu ya yi alkawarin za ta samar.

Ministan makamashi, Adebayo Adelabu da ya bayyana haka, ya kara da cewa wadatar wutar lantarki da yan kasa su ka samu ne ya sa ba su damu da karin farashin man fetur da aka yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.