Jami'an Hukumar Hisbah a Kano Za Su Warwasa, An Gabatar da Kudiri a Majalisa
- Majalisar dokokin Kano ta yaba da ayyukan ƴan Hisbah, ta fara kokarin ƙara masu albashi da alawus-alawus duk wata
- Ɗan majalisa mai wakiltar Minjibir, Abdulhamid Abdul ya gabatar da kudirin da ya nemi a maida ƴan Hisbah cikin ma'aikatan gwamnati
- Ya ce rundunar Hisbah ta Kano na taka muhimmiyar rawa wajen tsaftace jihar daga munanan ɗabi'u da kuma gyara tarbiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Majalisar dokokin Kano ta ce za ta yi duk mai yuwuwa wajen inganta walwala da jin daɗin jami'an hukumar Hisbah ta jihar.
Ɗan majalisa mai wakiltar Minjibir, Alhaji Abdulhamid Abdul ne ya faɗi hakan a lokacin da ya karɓi bakuncin mataimakin kwamandan Hisbh, Dr Mujahideen Abubakar.
Kamar yadda Leadership ta ruwaito, ɗan majalisar ya gana da mataimakain kwamandan ƴan Hisbah a zauren majalisa ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Majalisa na shirin inganta Hisbah
A kwanakin baya Albdulhamid Minjibir ya gabatar da kudiri a gaban majalisar dokokin Kano, wanda ya nemi a ƙara albashi da alawus-alawus na ƴan Hisbah.
Kudirin ya kuma bukaci majalisar da duba yiwuwar shigar da hukumar Hisbah cikin ma'aikatan gwamnati domin inganta aikinta na gyaran tarbiyya.
Hon. Abdulhamid Minjibir ya gabatar da wannan kudiri ne ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024.
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa duba da muhimman ayyukan hukumar, majalisar za ta yi wa dokar kafa Hisbah garambawul, daga bisani kuma gwamnati ta zartar.
Hukumar Hisbah ta lashi takobin tsaftace Kano
A nasa jawabin mataimakin kwamandan hukumar Hisbah, Mujahideen Abubakar ya yabawa dan majalisar bisa hangen nesan da yayi wajen gabatar da kudirin.
Ya yi nuni da cewa hukumar Hisbah ta Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta tsaftace jihar daga dukkan munanan dabi’u da gyaran tarbiyya.
Ƴan Hisbah sun lalata barasar N500m
A wani rahoton kuma hukumar Hisbah a jihar Kano ta lalata kayayyakin barasa da suka kai darajar Naira miliyan 500.
Hisbah ta bayyana cewa, wannan ya faru ne a kokarinta na tabbatar da bin dokar haramta shigowa, siyarwa da kwankwadar barasa a jihar Kano.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng