Da Gaske Alaka Ta Yi Tsami Tsakanin Majalisar Tarayya da Tinubu? An Samu Bayanai
- Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan rade-radin cewa akwai matsala tsakanin bangaren zartarwa dana dokoki
- Hadimin shugaban kasa, Bola Tinubu a bangaren Majalisa, Sanata Basheer Lado ya ƙaryata labarin da ake yadawa
- Hakan ya biyo bayan rahotanni da ke yawo cewa ana ƙoƙarin tsige shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Wasu na ta yada jita-jitar cewa an fara samun matsala tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Majalisar tarayya.
Sai dai hadimin shugaban a bangaren Majalisar dattawa, Sanata Basheer Lado ya musanta labarin da ake yadawa.
Rade-radin matsala tsakanin Tinubu da Majalisa
Basheer Lado ya ce akwai alaka mai karfi tsakanin Majalisar da bangaren zartarwa sabanin maganganun da ake yi, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan na zuwa ne bayan yada jita-jitar cewa jami'an DSS sun mamaye Majalisar domin dakile shirin tsige shugabanta, Godswill Akpabio.
Babu zancen tunbuke Godswill Akpabio a majalisa
Ana zargin rashin jituwa tsakanin Tinubu da Majalisar ne ya jawo haka, har ta kai wasu sanatoci ke neman tsige Akpabio.
Daga bisani, shugaban Majalisar, Akpabio ya karyata rade-radin inda ya ce babu wani shirin tsige shi.
Akpabio ya tura lamarin ga kwamitin ayyuka na musamman domin bincike tare da kawo rahoto kan lamarin.
'Babu matsala tsakanin Tinubu da Majalisa ' - Lado
Har ila yau, hadimin Tinubu a Majalisar, Sanata Lado ya ƙaryata labarin, ya bukaci al'umma su yi watsi da jita-jitar.
Lado ya ce wasu ne ke son kawo tarnaki game da alakar da ke tsakanin bangaren zartarwa da dokoki, cewar rahoton VON.
"Ina mai tabbatar muku labarin kanzon kurege ne, babu matsala a Majalisar Dattawa kamar yadda ake yadawa."
"Majalisar na cigaba da kasancewa cikin hadin kai domin tabbatar da martabar dimukraɗiyya a Najeriya."
"Bola Tinubu ya himmatu wurin tabbatar an samu alaka mai kyau a tsakani domin gina kasa baki daya."
- Sanata Basheer Lado
Majalisa ta yi albishir game da tsadar mai
Mun ba ku labarin cewa Majalisar Dattawa ta ce kamata ya yi kasuwar fetur ta rika yi wa kanta farashi tun bayan janye tallafi a bangaren.
Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce su na sa ido kan karin farashin da halin da jama'ar gari ke ciki kuma za a dauki mataki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng