Majalisa Ta ba Gwamnati Shawarar Hanyar da Za a Samu Saukin Tsadar Fetur

Majalisa Ta ba Gwamnati Shawarar Hanyar da Za a Samu Saukin Tsadar Fetur

  • Majalisar wakilan tarayya ta buƙaci a gyara matatun mai na ƙasar nan da suka lalace har aka daina amfani da su
  • Ƴan majalisar sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba da umarnin sauya ƙarin da aka yi kan farashin man fetur
  • Ƴan majalisar sun kuma buƙaci gwamnatocin jihohi da su kawo tsare-tsaren da za su ragewa mutanensu raɗaɗin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar wakilai ta yi magana kan tsadar man fetur da ake fama da ita a ƙasar nan.

Majalisar wakilan ta buƙaci kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), ma’aikatar albarkatun man fetur da sauran hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta gyare-gyare da kula da matatun man ƙasar nan da suka lalace.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago sun cimma matsaya kan farashin kayan abinci

'yan majalisa sun bukaci a gyara matatun mai
Majalisar wakilai ta bukaci a gyara matatun mai Hoto: @HouseNGR
Asali: Facebook

Majalisar wakilan ta yi wannan kiran ne a yayin zamanta na ranar Laraba, 16 ga watan Oktoban 2024, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar wakilai ta ba gwamnati shawara

Majalisar ta ce yin hakan zai zama matakin rage dogaro da man fetur ɗin da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje.

Majalisar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta bayar da umarnin sauya ƙarin farashin man fetur da aka yi, ta ce ƙarin ya ƙara jefa ƴan Najeriya cikin wahala.

Majalisar ta kuma buƙaci gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakin daidaita farashin man fetur da iskar gas, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ƴan majalisa suna so a kawo mafita

Ƴan majalisar sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta binciko wasu hanyoyin samar da makamashi domin rage dogaro da fetur da iskar gas.

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Ministan Tinubu ya fadi dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka daina korafi

Ƴan majalisar sun ce akwai buƙatar gwamnatocin jihohi su kawo tsare-tsaren da za su ragewa mutanensu raɗaɗi, kamar janye haraji kan harkokin sufuri da kayayyakin da tsadar mai ya shafa.

Majalisa ta hango matsala kan tsadar fetur

A wani labarin kuma, kun ji majalisar wakilai ta bayyana cewa akwai babbar barazana ga zaman lafiya saboda karin farashin fetur.

Majalisar wakilan ta yi gargadin a kwana cikin shirin bore daga jama'a saboda wahalar da karin farashin ya jefa rayuwarsu a ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng