Jita Jitar Rashin Lafiyar Tinubu da Abubuwan da Suka Faru bayan Tafiyarsa Hutu

Jita Jitar Rashin Lafiyar Tinubu da Abubuwan da Suka Faru bayan Tafiyarsa Hutu

  • A ranar 2 ga watan Oktoba shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutun mako biyu Birtaniya domin yin wasu bukatu
  • Biyo bayan tafiyar shugaban kasar, mutanen Najeriya sun mayar da hankali kan wasu abubuwa da suke da alaka da shi
  • A wannan rahoton, mun tattaro muku abubuwa da suka ja hankalin yan Najeriya bayan tafiyar Tinubu hutu kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A yanzu haka shugaban kasa Bola Tinubu yana kasar Faransa cikin hotun mako biyu da ya dauka.

Abubuwa da dama sun faru a Najeriya tun bayan tafiyar shugaba kasa Bola Ahmed Tinubu hutu kasar waje.

Kara karanta wannan

An fayyace wanda ke rike da Najeriya bayan ficewar Tinubu da Kashim daga kasar

Shugaba Tinubu
Abubuwan da suka faru bayan tafiyar Tinubu hutu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Mun tatttaro muku abubuwan da suka fi jan hankalin yan Najeriya bayan ɗaukar hutun da Bola Tinubu ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da suka faru bayan tafiyar Tinubu

1. Jita jitar rashin lafiyar Tinubu

Kwanaki kadan da tafiyar shugaba Bola Ahmed Tinubu hutu wasu yan Najeriya suka rika yada jita jitar cewa ba shi da lafiya.

Duk da yawan maganganun da al'ummar ƙasar suka yi, fadar shugaban kasa ba ta ce uffan ba kan jita jitar.

Sai dai akwai wasu da suka kai masa ziyara a Birtaniya wanda hakan ya nuna jita jitar ba ta da asali bare tushe.

2. Tafiyar Tinubu Faransa

Ana cikin raɗe radin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ba shi da lafiya a Birtaniya sai aka ji cewa zai wuce Faransa.

Yan Najeriya sun yi ta ce-ce-ku-ce kan lamarin inda wasu suke cewa ai bai kamata ya tafi wata ƙasa ba tunda ya dauki hutu zuwa Birtaniya.

Kara karanta wannan

T-Pain da sauran sunaye 4 da aka lakawa Tinubu da dalilan alakanta shi da su

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa fadar shugaban kasa ta yi martani kan lamarin inda ta ce Bola Tinubu yana da yancin tafiya duk inda ya so cikin hutunsa.

3. Karin kudin man fetur

Kwanaki kadan da tafiya hutun shugaba Bola Tinubu aka wayi gari da karin kudin fetur inda litar mai ta haura N1,000 a mafi yawan jihohi.

Lamarin ya tayar da kura kasancewar al'umma na fama da wahalar rayuwa kuma suna kira a rage kudin mai.

A wata tafiya da Bola Tinubu ya yi zuwa China ma dai an kara kudin fetur kafin ya dawo Najeriya.

4. Kiran Tinubu da T-Pain

Duk da cewa tun kafin tafiya hutu Birtaniya wasu yan Najeriya ke kiran Tinubu da T-Pain amma abin ya karu bayan tafiyarsa.

Hakan kuma ya faru ne bayan babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar ya kira shi da T-Pain a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake magana kan tallafin mai, ya yi albishirin samun sauki

Atiku Abubakar ya wallafa cewa duk wahalar da ake fama da ita a Najeriya Bola Tinubu ya kara kudin mai kamar bai damu da al'umma ba.

5. Tafiyar Kashim Shettima zuwa Sweden

A ranar 16 ga Oktoba fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Kashim Shettima zai tafi taro kasar Sweden.

Kasancewar shugaban kasa ya tafi hutu waje lamarin ya sanya yan Najeriya cece-ku-ce kan barin kasar a haka.

Sai dai jaridar Punch ta wallafa cewa fadar shugaban kasa ta ce babu wata matsalar shugabanci da za a fuskanta a kan tafiyar ta su.

Majalisa ta gardagi Bola Tinubu

Legit ta ruwaito cewa majalisar wakilai ta gargaɗi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 mai kamawa.

Yan majalisar wakilai sun bukaci gabatar da kasafin kudin cikin gaggawa inda suka ce ba za su amince da jinkiri ba a wannan karon.

Sun ce za su iya kin karɓar kasafin kudin idan shugaba Bola Ahmed Tinubu bai gabatar musu da shi a kan lokaci ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng