"Za a Samu Matsala:" Majalisa Ta Hango Barazanar Tashin Hankali kan Tsadar Fetur

"Za a Samu Matsala:" Majalisa Ta Hango Barazanar Tashin Hankali kan Tsadar Fetur

  • Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana fargabar karuwar tashe-tashen hankula biyo bayan karin da aka samu na farashin fetur
  • Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda ya gabatar da kudurin neman gwamnati ta shiga lamarin karin farashin
  • Majalisar ta shawarci gwamnatin tarayya ta lalubo hanyar magance matsin rayuwa da jama'ar kasar ke ciki kafin a samu matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta bayyana cewa akwai babbar barazana ga zaman lafiya a fadin kasar nan sakamakon karin farashin fetur.

A zamanta na ranar Laraba, majalisar ta yi gargadin a kwana cikin shirin bore daga jama'a saboda wahalar da karin farashin ya jefa rayuwarsu a ciki.

Kara karanta wannan

Farashin man fetur na iya sauka yayin da Majalisa ta sa baki kan ƙarin da aka yi

Majalisa
Majalisa ta yi gargadin karuwar tashin hankali kan farashin fetur Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gargadin majalisar na zuwa a daidai lokacin da jagororin kungiyar kwadago da gwamnati su ka zauna domin duba batun farashin fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta yi tir da karin farashin man fetur

Tashar Arise News ta wallafa cewa majalisar wakilan kasar nan ta yi Allah wadai da karin farashin litar fetur da aka yi a kasar nan, wanda ya kara dagula lamura.

Majalisar ta bukaci gwamnati ta gaggauta daukar matakan sauko da farashin domin kare afkuwar tashe-tashen hankula a kasa.

Tsadar fetur: Majalisa nemi daukin gwamnati

Majalisar wakilai ta shawarci gwamnatin tarayya ta duba halin matsin tattalin arziki da jama'a su ke ciki domin daukar matakan kawo sauki.

Kiran ya biyo bayan kudurin gaggawa da shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda ya gabatar da goyon bayan akalla yan majalisa 100.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kadu da faduwar tankar fetur a Jigawa, an fadi matakin da za a dauka

'Yan Majalisa sun sa baki kan farashin fetur

A wani labarin, kun ji cewa majalisar wakilai ta shiga batun karin farashin man fetur bayan kamfanin NNPCL ya kara farashin kowace lita zuwa sama da N1,000 a dukkanin gidajen mansa.

A zaman majalisar na ranar Laraba, an bukaci gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin domin soke farashin da aka kara a kwanan nan tare da lalubo hanyar saukakawa jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.