Gwamnan APC Ya Ciri Tuta, Ya Sanar da Sabon Albashin da Zai Fara Biyan Ma'aikata
- Gwamnan jihar Legas ya yi alƙawarin biyan ma'aikata N85,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi nan ba da daɗewa ba
- Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba, 2024
- Babajide Sanwo-Olu ya zama gwamna na farko da ya yi alƙawarin kai albashi mafi karanci N100,000 a shekarar 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta biya N85,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Gwamnan ya sanar da haka ne ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba, 2024, inda ya ce nan da wasu ƴan watanni zai ƙara albashin zuwa N100,000.
Babajide Sanwo Olu ya bayyana haka ne a wata hira da gidan talabijin na Channels tv ranar Laraba wanda wani ya wallafa a dandalin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Legas ya haura albashin N70,000
Idan ba ku manta ba gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa.
Amma bayan haka wasu jihohin sun yi ƙari a kan haka domin inganta walwala da jin daɗin ma'aikatan gwamnati.
Da yake jawabi, Gwamna Sanwo-Olu ya ce gwamnatinsa a shirye take ta kara mafi karancin albashi zuwa N100,000 a watan Janairun 2025.
Gwamnan ya ce ma'aikata sun cancanci a rika biyansu albashin da zai ɗauke ɗawainiyar su da ta iyalansu a wata.
Gwamna Sanwo-Olu zai fara biyan ma'aikata N85,000
Sanwo-Olu ya ce:
"Dangane da mafi karancin albashi da na ji kun ambata, ina mai farin cikin sanar da cewa mu da ƴan kwadago mun cimma matsayar biyan N85,000."
"Wannan ba wani abu ba ne, ba zan tsaya ina cewa muna biyan albashi fiye da wasu jihohi ba, magana ce ta gwargwadon abin da kowa zai iya."
Majalisa ta dakatar da ciyaman a Legas
A wani labarin kuma majalisar dokokin jihar Legas ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Alimosho, Jelili Sulaimon, daga kan muƙaminsa.
A cewar ƴan majalisar, dakatarwar da aka yi wa shugaban ƙaramar hukumar za ta fara aiki ne nan take ba tare da ɓata wani lokaci ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng