An Fayyace Wanda Ke Rike da Najeriya bayan Ficewar Tinubu da Kashim daga Kasar

An Fayyace Wanda Ke Rike da Najeriya bayan Ficewar Tinubu da Kashim daga Kasar

  • Yayin da ake korafi kan wanene zai jagoranci Najeriya bayan shugaba da mataimakinsa sun bar kasar, an samu martani
  • Fadar shugaban kasa ta fayyace yadda lamarin ya ke bayan Kashim Shettima ya fice zuwa kasar Sweden domin halartar taro
  • Hakan na zuwa ne yayin da Bola Tinubu yake Faransa wanda ake kokwanton waye zai mulki kasar bayan Shettima ya fice

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi magana bayan korafi da tunanin wanda zai jagoranci Najeriya.

Hakan ya biyo bayan tafiya Sweden da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yi a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024.

An fadi wanda ke mulkin Najeriya bayan tafiyar Kashim Shettima kasar Sweden
Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan korafi game da tafiyar Kashim Shettima kasar Sweden. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Kashim Shettima.
Asali: Facebook

Gwamnati ta magantu da Shettima ya tafi Sweden

Kara karanta wannan

Ana kewar rashin Tinubu, Shettima zai shilla ketare, an samu bayanin tafiyar

Hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga ya fayyace komai yayin Bola Tinubu ke Faransa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya ce babu wani rikitarwa kan wa zai riƙe ƙasar duk da Bola Tinubu da Kashim ba su Najeriya a yanzu.

Ya ce Tinubu da ke Faransa yana cigaba da ba da umarni da kuma amsa kiraye-kiraye kan abin da ke gudana a Najeriya.

Abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce

Har ila yau, Onanuga ya ce a kundin tsarin mulkin Najeriya babu inda aka ce sai dole shugaba yana Najeriya a bayyane kafin ya yi mulki.

"Ya kamata a sani shugaban kasa da mataimakinsa sun tafi ne domin kawo sauyi ga Najeriya, duk da ba su gida babu matsala kan shugabancin kasar."
"Ma'aikatu na aiki babu matsala, shugaban Majalisar Dattawa sakataren Gwamnatin Tarayya da hafsoshin tsaro da manyan ma'aikatu suna aiki ba tare da matsala ba.

Kara karanta wannan

T-Pain da sauran sunaye 4 da aka lakawa Tinubu da dalilan alakanta shi da su

"Haka ya faru a 2022 da shekarar 2023 a mulkin Muhammadu Buhari lokacin da ya bar Najeriya kuma mataimakinsa, Yemi Osinbajo shi ma ya bar kasar."

- Bayo Onanuga

Shettima ya shilla zuwa kasar Sweden

A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima zai tafi Sweden domin wakiltar Najeriya a wasu muhimman abubuwa.

Kashim Shettima zai ziyarci kasar Sweden domin tattaunawa game da wasu lamura masu muhimmanci saboda a kawo sauyi a kasar.

Wannan na zuwa yayin da ake dakon dawowar Bola Tinubu da ke Faransa bayan barin Burtaniya a cikin kwanakin nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.