Gwamnan PDP Ya Umarci Biyan Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 Nan Take

Gwamnan PDP Ya Umarci Biyan Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 Nan Take

  • Gwamna Sheriff Oborevwori na Delta ya umarci fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 ga mafi ƙanƙantan ma'aikatan jihar
  • Gwamna Sheriff ya ba da umarnin biyan ne nan take wanda za a fara ba ma'aikata a karshen watan Oktoban 2024 da muke ciki
  • Sakataren gwamnatin jihar ya tabbatar da haka, ya ce gwamnan ya duba halin da al'umma ke ciki ne na tsadar rayuwa a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Delta - Gwamnatin jihar Delta ta shirya biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ma'aikata.

Gwamna Sheriff Oborevwori shi ya ba da umarnin fara biyan albashin a karshen watan Oktoban 2024.

Gwamna ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi
Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya umarci fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000. Hoto: Sheriff Oborevwori.
Asali: Facebook

Gwamna ya ba da umarni kan albashin N70,000

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Jerin gwamnonin da za su biya ma'aikata fiye da N70000

Vanguard ta ce gwamnan ya bayyana haka bayan ganawa da kungiyoyin NLC da TUC a birnin Asaba a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin jihar, Dakta Kingsley Emu ya tabbatar da umarnin gwamnan a yau Laraba 16 ga watan Oktoban 2024.

Emu ya ce an gudanar da ganawar inda gwamna Sheriff ya bukaci biyan albashin a karshen watan Oktoba da muke ciki, cewar TheCable.

Halin kunci: Gwamna zai biya albashin N70,000

"Kwamitin biyan albashin tun farko ya ce ba zai biya mafi ƙarancin albashi ba sai ya samu tsarin hukumar NISWC."
"A yanzu kwamitin ya gama duba kan tsarin biyan albashin daga NISWC game da yadda aka kasafta biyan kuɗin."
"Duk da ba mu gama duba kan sauye-sauyen ba, gwamnan ya umarci fara biyan saboda halin da al'umma ke ciki."

- Kingsley Emu

Kara karanta wannan

Gwamma ya amince da N77,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata

Gwamna Inuwa zai biya mafi ƙarancin albashi

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya amince da biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ma'aikata.

Inuwa a kwanakin baya, ya bayyana cewa ba zai iya biyan mafi ƙarancin albashin ba inda ya ce da kyar ake biyan N30,000 a Gombe.

Amma a yanzu gwamnan ya lashe amansa inda ya rattaba hannu kan sabon albashin na N71,451 ga ma'aikata har da na ƙananan hukumomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.