N195/lita: Yadda Tinubu Ya Karya 'Alkawari' kan Farashin Fetur Sau 4 a Kasa da Shekaru 2

N195/lita: Yadda Tinubu Ya Karya 'Alkawari' kan Farashin Fetur Sau 4 a Kasa da Shekaru 2

Gabanin zaben 2023, shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki alkawarin duba farashin da yan kasar nan ke sayen kowace litar domin a samu ragi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

A shekarar 25 Janairu, 2023 ne shugaban kasa na yanzu ya koka kan yadda yan kasar nan ke sayen litar fetur a kan N195.

Tinubu
An samu hauhawar farashin litar fetur sau 4 bayan hawan Tinubu mulki Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Wannan ta sa Bola Ahmed Tinubu ya lashi takobin dakatar da tashin farashin litar fetur zuwa kar ya kai N200, sannan a sauko da farashin daga N195.

A wanna rahoto, za ku ji yadda shugaban ya gaza cika alkawari har ma da yadda aka samu hauhawar farashin fetur a kasar nan.

Kara karanta wannan

Kwamitin Tinubu ya waiwayi masu kudi, ana shirin laftawa attajirai haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. An kara farashin fetur tashin farko

Yan Najeriya sun sha mamaki a lokacin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana janye tallafi man fetur a ranar da ya sha rantsuwar kama aiki.

Nigerian Tribune ta tattaro cewa Tinubu na ayyana janye tallafin fetur ranar 29 Mayu, 2024, inda farashin kowace lita ya haura zuwa N448 - N557.

2.Yuni 2023: Farashin fetur ya kara sama

Jama'a ba su kammala farfadowa daga karin da aka yi a watan da ya gabata ba, sai aka samu karuwar farashin litar fetur.

A wancan lokaci, an samu karin 10.77% a kan yadda ya ke a watan Mayu 2023, inda kowace lita ta tashi daga N557 - N617.

3. Satumba 2024: Farashin fetur ya haura N800

A watan Satumba na shekarar nan ne aka kara samun hauhawar farashin litar fetur, inda ya koma daga tsakanin N855- N897, wato an samu karin da 45.38%.

Kara karanta wannan

Ana kokarin shawo kan tsadar fetur, farashin gas din girki ya lula sama

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya fito ya kare kansa da cewa ya na fuskantar matsi sakamakon tarin bashi da ke barazana ga wadatar fetur.

4. NNPCL ya kara farashin fetur a Oktoba

Jaridar Punch na daga jaridun da su ka wallafa labarin karin farashin litar fetur a watan Oktoba 2024, kamfanin NNPCL ya kara farashi a dukkanin gidan mansa.

Karin farashin litar fetur ya hau zuwa N1,030 kowace lita yayin da aka samu sauyi a wasu wuraren farashin ya haura haka.

Kila farashin litar fetur ya sauka

A baya mun ruwaito cewa ana sa ran farashin litar man fetur da ya haura N1,000 a fadin kasar nan zai iya saukowa bayan majalisar wakilai ta tsoma baki.

A zaman da majalisar ta yi a ranar Laraba, ta nuna rashin goyon bayanta kan karin, ta bukaci a gaggauta sassauta farashin lita domin jama'a su sarara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.