Matsin Rayuwa: Gwamnati za Ta Turawa Talakawan Najeriya Kudi ta Asusun Banki

Matsin Rayuwa: Gwamnati za Ta Turawa Talakawan Najeriya Kudi ta Asusun Banki

  • Gwamantin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bayyana ƙoƙarin da take wajen rage raɗaɗin wahalar rayuwa ga yan Najeriya
  • Ministan tattalin arziki ya bayyana shirin tallafawa miliyoyin talakawa da kudi ta asusun banki domin rage matsin rayuwa
  • Legit ta tattauna da wani dan asalin jihar Gombe kan sabon alkawarin da fadar shugaban kasa ta yi wa yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ministan kudi ya yi albishir ga talakawa kan shirin rage radadin rayuwa na gwamnatin Bola Tinubu.

Wale Edun ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya tana kokari wajen ganin al'umma sun samu sauƙin rayuwa a Najeriya.

Bola Tinubu
Gwamnati za ta raba rallafin kudi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa Wale Edun ya ce miliyoyin yan Najeriya ne za su samu tallafin kudi ta asusun bankinsu.

Kara karanta wannan

Bankin duniya ya ba gwamnatin Tinubu shawara kan maido tallafin man fetur

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a rabawa talakawa kudi ta banki

Ministan kudi ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta shirya domin turawa talakawan Najeriya kudi ta asusun banki domin rage radadin rayuwa.

Wale Edun ya ce ana sa ran kashi 60% na talakawan Najeriya ne za su samu tallafin kudin da za a tura ta asusun banki.

Mutane nawa ne za su samu tallafin?

The Sun ta wallafa cewa Edun ya ce a nan gaba kadan za a fara tallafawa gidaje miliyan 15 ne da kudin wanda za su kai mutum miliyan 20.

Ministan ya tabbatar da cewa wannan na cikin hanyoyin da shugaban kasa Bola Tinubu ke bi wajen kashe kudin da gwamnatin tarayya ta samu.

Gwamnati na kokarin rage tsadar abinci

Wale Edun ya bayyana cewa gwamantin Bola Tinubu tana kokarin fadada hanyar samar da abinci domin rage tsadarsa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya juyawa Tinubu baya, ya ce manufofinsa ne suka kawo yunwa

Ya tabbatar da cewa za su wadatar da yan Najeriya da abinci sosai ta yadda kowa zai iya saye domin rage tsadar rayuwa.

Legit ta tattauna da Mu'azu

Wani dan asalin jihar Gombe, Mu'azu Abdullahi ya zantawa Legit cewa zai yi farin ciki idan talakawa suka samu hanyar rage radadin rayuwa.

Sai dai duk da haka Mu'azu ya ce babban abin da zai amfani talakawa shi ne maido tallafin fetur da gwamnati ta cire.

An fara raba tallafin ambaliyar ruwa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta fara raba tallafin ambaliyar ruwa ga dubban al'ummar jihar.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce za a raba tallafin kudi da kayan gini ga nau'ukan waɗanda ambaliyar ruwa ta musu barna a bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng