An Fara Raba Tallafin Ambaliyar Ruwa, Mutane Za Su Samu N600,000
- Gwamnatin Katsina ta sanar da karbar tallafin kudi daga shugaban kasa Bola Tinubu, a rabawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa an ware gidaje da mutanen da za su mori tallafin a dukkan sassan jihar Katsina
- Haka zalika Dikko Umaru Radda ya bayyana yadda za a raba kudin da abin da za a ba nau'ukan waɗanda ambaliyar ta shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Gwamna Dikko Umaru Radda ya tabbatar da karbar tallafin ambaliyar ruwa na N3bn daga gwamnatin tarayya.
Gwamna Dikko Radda ya tabbatar da cewa za a raba tsabar kudi da kayan gini ga wadanda ambaliya ta shafa a jihar.
Hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ne ya wallafa yadda za a raba kudin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tallafin wadanda ruwa ya rusawa gidaje
Gwamnan jihar Katsina ya ce an ware mutane 439 da ambaliyar ruwa ta rusa musu gidaje gaba daya.
Wadanda gidajensu suka rushe gaba daya za a ba su tallafin tsabar kudi har N600,000 ga kowane ɗaya daga cikinsu.
Tallafin wadanda ruwa ya yi wa barna sosai
Haka zalika gwamnatin Katsina ta ware mutane 628 da ruwa ya musu barna sosai a gidajensu amma bai gama rusawa ba.
Gwamna Dikko Radda ya tabbatar da cewa wadannan nau'in za a ba kowane ɗaya daga cikinsu tallafin kudi N300,000.
Sauran wadanda za a ba tallafin ambaliya
Gwamnatin Katsina ta kare ware N200m wajen sayan kayan gini da za a raba ga mutane 1,772 da ruwan ya yi wa barna amma ba sosai ba.
Ambaliyar ruwa a jihar Katsina ta shafi gidajen al'umma, gonaki da wuraren sana'o'i da dama wanda hakan ya jefa mutane cikin damuwa.
Ambaliya ta ci gidaje a Kogi
A wani rahoton, kun ji cewa ambaliyar ruwa ta ci garuruwa da dama a kananan hukumomin jihar Kogi, kimanin mutane miliyan biyu sun rasa gidajensu.
Gwamnatin jihar Kogi ta buƙaci a kawo mata ɗauki domin tallafawa waɗanda wannan mummunan ibtila'i ya rutsa da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng