Daidaiton Jinsi: Tinubu Ya Bayyana Babban Kudurin Gwamnatinsa kan Matan Najeriya

Daidaiton Jinsi: Tinubu Ya Bayyana Babban Kudurin Gwamnatinsa kan Matan Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta jajirce wajen karfafa ci gaban mata da kuma daidaiton jinsi
  • Tinubu ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa a wajen taron kaddamar da shirin 'A bunkasa ta' na ma’aikatar harkokin mata
  • Shugaban ya bukaci gwamnati da masu zaman kansu da su hada karfi da karfe wajen karfafa mata domin ci gaban al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Talata, Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a kara daukar matakai domin tabbatar da karfafa gwiwar mata a Najeriya.

Tinubu ya bayyana haka ne a wajen wata liyafar cin abinci na tara kudade da ma’aikatar harkokin mata ta tarayya ta shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

An fadawa Tinubu ministan da zai kora yayin da 'yan Najeriya ke kwana a duhu

Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan karfafa mata a wani taro a Abuja
Tinubu ya jaddada kudurin gwamnatinsa na karfafa ci gaban mata da daidaiton jinsi. Hoto: @AjuriNgelale
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta rahoto cewa George Akume, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ne ya wakilci shugaban kasar a wajen taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin gwamnati na daidaiton jinsi

Taken taron shi ne: "A bunkasa ta: Najeriya ta zamo kasar da mata za su shiga harkar noma, kiwon lafiya, shari'a, nishadi da samun ci gaba."

Tinubu ya ce taron ya nuna wani gagarumin ci gaba a tafiyar gwamnatinsa na tabbatar da daidaiton jinsi da kuma ci gaban mata mai dorewa.

Shugaban kasar ya ce karfafa mata yana da muhimmanci ga ci gaban kasa inda ya nemi hadin kai tsakanin gwamnati da bangarorin masu zaman kansu domin cimma hakan.

'Dole mu karfafa ci gaban mata’ - Tinubu

Jaridar Arise ta ruwaito shugaban kasar ya shaida cewa:

“A kokarinmu na tabbatar da adalci da daidaito, dole ne mu tabbatar da cewa mata sun samu adalci da kuma kariya daga duk wani nau’in tashin hankali da wariya.

Kara karanta wannan

Kwamitin Tinubu ya waiwayi masu kudi, ana shirin laftawa attajirai haraji

“Dole ne mu karfafa mata ba wai don ci gabansu kadai ba, har ma da ci gaban al’ummarmu baki daya. Idan dai muka karfafa iyalai, to tamkar mu karfafa al'umma ne baki daya."

Hamshakin attajirin nan, Arthur Eze ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 100 domin tallafawa shirin 'A bunkasa ta.'

'Mata sun cancanci mukamai' - Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta koka kan yadda ta ce an mayar da mata saniyar ware a rabon mukaman gwamnati.

Sanata Tinubu, ta bayyana cewa mata sun cancanci a basu karin mukamai a matakan gwamnati daban daban domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.