"Najeriya ba Talakar Kasa ba ce:" Kwamitin Tinubu Ya Gano Dalilin Rashin Kudi

"Najeriya ba Talakar Kasa ba ce:" Kwamitin Tinubu Ya Gano Dalilin Rashin Kudi

  • Kwamitin gwamnatin tarayya kan tsare-tsare da yi wa harkokin haraji garambawul ya bayyana cewa kasar nan na da arziki
  • Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ne ya sanar da haka, inda ya ce babu kamshin gaskiya cikin labarin cewa kasar nan ba ta da kudi
  • Amma ya bayyana dalilin da ya sa kasar ke rashin kudi, wanda ya ce gwamnati na lalubo hanyar magance matsalolin da ake fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja- Shugaban kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da garanbawul ga harkokin haraji , Taiwo Oyedele ya musanta cewa kasar nan ba ta da kudi.

Kara karanta wannan

Kwamitin Tinubu ya waiwayi masu kudi, ana shirin laftawa attajirai haraji

Ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a taron kasa kan tabbatar da kudin shiga ga gwamnati a Abuja.

Tinubu
Kwamitin shugaban kasa ya ce akwai kudi a kasar nan Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Arise TV ta tattaro cewa Mista Taiwo Oyedele ya ce babu kamshin gaskiya a cikin rade-radin da wasu ke yi na cewa kasar nan na cikin talauci tsundum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamitin Tinubu ya gano dalilin 'talauci'

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da garanbawul ga harkokin haraji ya gano dalilin da ya sa ake ganin Najeriya ba ta da kudi.

Shugaban Kwamitin, Taiwo Oyedele ya ce kasar na fama da matsalar zurarewar kudin shiga da ake samu, wanda ke jawo asarar kudaden kasar.

Gwamnatin Tinubu za ta magance talaucin Najeriya

Mista Taiwo Oyedele ya bayyana cewa yanzu haka gwamnati na kokarin nemo dabarun hana zurarewar kudin shigarta da tabbatar da tsare kadarorin da ta ke da su.

Kara karanta wannan

"Wahala a Najeriya:" Bankin Duniya ya yabi Tinubu, ya ba Shugaban kasa shawara

Ya kara da cewa mafi yawan harajin da kasar nan ke samu ana karbo shi ne daga talakawa, saboda haka dole a kare martabarsu da kudinsu.

Kwamitin Tinubu na son a kara haraji

A wani labarin kun ji cewa kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsare da garanbawul ga harkokin haraji ya fara mika bukatar kara haraji da ake karba daga masu kudi a fadin kasar nan.

A kudurin da ake fatan majalisa ta amince da shi, duk wanda ya ke samun sama da Naira miliyan 1.5 a wata zai rika biyan gwamnatin tarayya haraji wanda ya kai 25% na abin da ya ke samu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.