Sanata Ya Fallasa Rawar da 'Yan Siyasa Ke Takawa kan Shan Miyagun Kwayoyi
- Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya zargi ƴan siyasa da ɗora matasa a kan harkar shan miyagun ƙwayoyi
- Sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu ya ce ƴan siyasan na ɗora matasan ne kan harkar domin cimma manufofinsu
- Ya bayyana cewa wasu ƴan siyasan har ajiye miyagun ƙwayoyin suke yi a gidajensu domin rabawa lokacin zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce dole ne ƴan siyasa su ɗauki kaso mai tsoka na laifin yawaitar shan miyagun ƙwayoyi a ƙasar nan.
Kawu Sumaila na jam'iyyar NNPP ya zargi ƴan siyasa da ɗora matasa kan harkar shan miyagun ƙwayoyi.
Sanatan ya kuma zargi ƴan siyasa da ƙarfafawa matasa gwiwa su yi shaye-shaye domin su riƙa yi haramtattun ayyuka a madadinsu da sunan siyasa, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata ya zargi ƴan siyasa kan shan miyagun ƙwayoyi
Kawu Sumaila ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana kan muhawarar da ake yi kan ƙudirin dokar kafa hukumar wayar da kai kan shan miyagun ƙwayoyi a zauren majalisar dattawa.
A cewar sanatan mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu, ƴan siyasa suna tara miyagun ƙwayoyi a gidajensu, sannan kuma suna bayar da kuɗi domin sayo su musamman a lokutan zaɓe.
Kawu Sumaila ya ƙalubalanci sanatoci
Ya ƙauracewa bayar da takamaiman misalai ko sunayen ƴan siyasa masu ɗora matasa kan harkar shan miyagun ƙwayoyi.
"Mutum nawa ne a nan za su iya rantsuwa da Alkur’ani ko littafi mai tsarki cewa ba su goyon bayan ayyukan da suka shafi shan miyagun ƙwayoyi a cikin al’ummarsu? Mu nawa ne?"
- Abdulrahman Kawu Sumaila
Gwamnatin Kano ta waiwayi dillalan miyagun ƙwayoyi
A wani labarin kuma, kun ji gwamnatin Kano ta waiwayi dillalan miyagun kwayoyi, musamman wadanda ke neman mafakar shari'a yayin da aka kwace haramtattun kayansu.
Gwamna Abba Yusuf ya yi mamakin irin karfin halin wasu dillalan kwayar, wadanda ke zuwa kotu su karbo takardar izinin a saki kayansu da aka kwace.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng