Yan Bindiga Sun Yi wa Jama'a Barazana, Sun Sha Alwashin Kai Hari Zamfara
- Mazauna karamar hukumar Anka da kewaye a Zamfara sun nemi daukin gwamnati da jami'an tsaro kan barazanar kai masu hari
- Wasu isassun yan bindiga ne su ka gargadi mazauna yankin tare da barazanar cewa za a fatattake su a hanya da gonakinsu
- Gargadin harin mataki ne na ramuwar gayya biyo bayan kama wanda ke kai masu makamai da jami'an tsaron Zamfara su ka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Mazauna Anka a jihar Zamfara sun yi ihun neman dauki biyo bayan barazana da yan bindiga su ka yi na kai masu hari.
Yan ta'addan sun mika wa mazauna Anka gargadi, aka nemi su kwana da sanin za a kawo masu hare-hare a gonakinsu da sauran sassan karamar hukumar.
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa yan ta'addan sun mika gargadin ga mazauna karamar hukumar Anka a ranar 14 Oktoba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin yunkurin kai farmaki Zamfara
Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan na shirin kai hari a matsayin martani kan kama mai yi masu safarar makamai da jami'an tsaron Zamfara su ka yi.
Rahotanni sun tabbatar da damke Zayyanu Abdullahi, dan asalin yankin Shinkafi a Zamfara a hanyar Anka-Bagege dauke da alburusai masu tarin yawa.
Zamfara: An mika dan bindiga ga sojoji
Jami'an tsaron 'Zamfara State Community Protection Guard' sun mika dan aiken yan bindiga da aka kama ga jami'an sojojin da ke karamar hukumar Anka.
An gano cewa Zayyanu Abdullahi na yunkurin mika alburusan ga wasu yan ta'adda da ke kauyen Kawaye a lokacin da jami'an tsaron su ka yi ram da shi.
Yan ta'adda sun fafata a Zamfara
A baya kun ji cewa an samu sabani tsakanin wasu yan bindiga a jihar Zamfara, lamarin da ya yamutsa hazo har ta kai ga sun fafata tare da jawo asarar rayuka a tsakaninsu.
A yayin artabun, an kashe Kachalla Ibrahim Gurgun Daji, daya daga cikin fitinannun yan ta'adda da su ke jagorantar kai farmaki kauyuka da dama a Zamfara da kewaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng