An Yi Artabu Tsakanin Bangarori 2 na Yan Bindiga da Suka Farmaki Sakatariyar APC

An Yi Artabu Tsakanin Bangarori 2 na Yan Bindiga da Suka Farmaki Sakatariyar APC

  • Miyagun yan bindiga sun kai wani hari a sakatariyar jam'iyyar APC da ke jihar Bayelsa a Kudancin Najeriya
  • Maharan sun shammaci al'umma ne lokacin da ake tsaka da gudanar da ganawa a sakatariyar da ke Yenagoa
  • Daga bisani, wasu yan bindiga sun fatattaki maharan kafin rundunar yan sanda ta kawo dauki a wurin da abin ya faru

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Bayelsa - Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindiga sun kai hari ofishin jam'iyyar APC a jihar Bayelsa.

Yan bindiga sun durfafi sakatariyar jam'iyyar ne da ke kan hanyar Melford Okilo da ke birnin Yenagoa.

Yan bindiga sun kai hari sakatariyar jam'iyyar APC
Yan bindiga sun kai hari sakatariyar APC da ke jihar Bayelsa. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yan bindiga sun kai hari sakatariyar APC

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ƙawanya a kauye cikin dare, sun kashe mutane

The Sun ta tabbatar da cewa maharan sun kai hari ne ana tsaka da ganawa kan rigimar jam'iyyar a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganawar na da nasaba da rigimar da ke faruwa wanda har ya sanya dakatar da wasu jiga-jiganta da dama a jihar.

Legit Hausa ta kawo musu labarin yadda shugaban jam'iyyar a karamar hukumar Ekeremor ya dakatar da karamin Ministan mai, Heineken Lokpobiri.

Bayan dakatar da Ministan, an kuma kori wasu jiga-jigai jam'iyyar ciki har da dan takarar gwamna a 2019, cewar rahoton Tribune.

Mahara suka tarwatsa yan bindiga a Bayelsa

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga ne suka tarwatsa maharan da suka zo sakatariyar tun farko.

Daga bisani, jami'an yan sanda sun samu isa wurin inda suka fatattaki duka yan bindigar tare da nasarar kama guda daya da ake zargi.

Jam'iyyar APC na fama da matsalar rikicin cikin gida a jihar Bayelsa da ke neman daidaita ta.

Kara karanta wannan

Wasu na gudun APC a Arewa, daruruwa sun watsar da PDP, sun bi sahun Ganduje

Dakatar da Minista ya yi sanadin shugaban APC

Mun ba ku labarin cewa shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Ekeremor l, Eniekenemi Mitin ya rasa mukaminsa saboda dakatar da Minista.

Mitin ya rasa kujerarsa ne bayan shugabannin jam'iyyar sun dauki matakin tuge shi kan wasu zarge-zarge masu girma da ake jefe shi da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.