Shekaru 2 da Hukuncin Kisa kan Kashe Hanifa, AbdulMalik Ya Nufi Babbar Kotu

Shekaru 2 da Hukuncin Kisa kan Kashe Hanifa, AbdulMalik Ya Nufi Babbar Kotu

  • Malamin nan da kotu ta yankewa hukuncin kisa bayan kama shi da laifin kashe dalibarsa, Hanifa Abubakar ya sake komawa kotu
  • Kotu ta yankewa AbdulMalik Muhammad Tanko da abokinsa, Hashimu Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe yarinyar
  • Amma mutanen biyu ta hannun lauyansu, Anthony Ezenwoko sun shigar da korafi kotun daukaka kara su na kalubalantar hukuncin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - AbdulMalik Muhammad Tanko, malamin da kotu ta kama da da laifin kashe dalibarsa mai shekaru biyar, Hanifa Abubabar ya koma kotu.

A ranar 28 Yuli ne babbar kotu mai zamanta a Kano ta kama AbdulMalik da abokinsa Hashimu Isyaku da laifin kashe dalibar, kuma mai shari'a Usman Mallam Abba ya yanke masu hukuncin kisa.

Kara karanta wannan

An kori yan sanda kan kitsa kashe dalibi yayin zanga zangar tsadar rayuwa

Hanifa
Makashin Hanifa ya kalubalanci hukuncin kisa da aka yi masa Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa AbdulMalik da Hashimu sun shigar da kara kotun daukaka kara, inda su ke neman a janye hukuncin kisa ta hanyar rataya da aka yanke masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin daukaka karar malamin Hanifa

Jaridar The Guardian ta wallafa cewa lauyan wadanda aka kama da laifi, Barista Anthony Ezenwoko ya ce kotu ta yanke hukunci bisa kuskure.

Ya bayyana cewa shaidun da aka gabatar a gabanta ba su tabbatar da cewa wadanda aka yi kara ne su ka kashe karamar yarinyar ba, saboda haka ana neman a janye hukuncin.

Yadda aka kama malamin Hanifa da laifi

Tun da baya, AbdulMalik, malamin yarinyar nan Hanifa Abubakar, da ita daya tilo iyayenta su ka haifa a lokacin ya amsa cewa da kansa ya kashe dalibar tasa.

Ya shaidawa yan sanda cewa ya dauke ne daga makarantar Islamiya ta Sheikh Dahiru Bauchi Islamic Foundation, ya kashe ta da shinkafar bera sannan ya binne ta a wata makaranta da ke karamar hukumar Nassarawa a Kano.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan zargin Hon. Doguwa da ake yi da kisan kai, an ci tarar Abba Kabir

Kisan Hanifa: Kotu ta yanke hukunci

A baya mun wallafa cewa babbar kotu da ke zamanta a Kano ta yanke hukunci kan mummunan kisa da aka yi wa daliba yar shekaru biyu da haihuwa, Hanifa Abuabakar a Kano.

Tun da fari, an gurfanar da AbdulMalik Tanko a gaban kotu bayan gano cewa ya na da hannu a cikin satar dalibarsa Hanifa tare da hadin bakin wasu mutane guda biyu domin yanke masu hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.