Matar Tsohon Gwamna a Najeriya Ta Yi Bankwana da Duniya

Matar Tsohon Gwamna a Najeriya Ta Yi Bankwana da Duniya

  • Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja ya yi babban rashi bayan rasuwar daya daga cikin matansa a jiya Litinin
  • Rahotanni sun tabbatar da rasuwar marigayiyar mai suna Tinuade Ladoja a jiya Litinin 14 ga watan Oktoban 2024
  • Marigayiyar ta rasa ranta ne tana da shekaru 71 a duniya bayan ta sha fama da jinya a birnin Ibadan da ke jihar Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - An shiga jimami bayan rasuwar matar tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja.

Marigayiyar mai suna Tinuade Ladoja ta rasu ne a jiya Litinin 14 ga watan Oktoban 2024 bayan fama da jinya.

Matar tsohon gwamna ta riga mu gidan gaskiya
Tsohon gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja ya tafka babban rashi na matarsa. Hoto: Ajibola Akinyefa.
Asali: Facebook

Matar tsohon gwamnan Oyo ta rasu

Kara karanta wannan

An rasa rayuka yayin da tireloli suka murkushe masu keke Napep

TheCable ta ruwaito cewa matar tsohon gwamnan, Tinuade ta rasa ranta tana da shekaru 71 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin tsohon gwamnan a bangaren yada labarai, Adeola Oloko shi ma ya tabbatar da labarin rasuwar marigayiyar ga jaridar Punch.

"Haka ne, an tabbatar da rasuwarta, ta rasu da gaske, muna addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama."

- Adeola Oloko

Yadda marigayiya Ladoja ta riƙe addininta

Kafin rasuwarta, tana daya daga cikin masu ruwa da tsaki a cocin Celestial Church of Christ da ke birnin Ibadan.

Har ila yau, cocin ya tabbatar da rasuwar marigayiyar a jiya Litinin 14 ga watan Oktoban 2024 a shafin Facebook.

"Cikin alhini da kunci tare da sallamawa ga ikon Ubangiji mu ke sanar da babban rashi da muka yi."
"Mu na samar da rasuwar daya daga cikin hazikan mambobinmu, Mama Tinuade Ladoja wacce ta rasu a ranar Litinin."

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da wani gini mai hawa 2 ya rufta, bidiyo ya bayyana

"Marigayiyar ta rasu tana da shekaru 71 a duniya, mu na jiran sanarwa ta musamman daga iyalanta, mu na addu'ar Ubangiji ya jikanta."

- Cewar sanarwar

Mahaifiyar tsohon gwamna ta kwanta dama

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Rabaran Jolly Nyame ya gamu da rashi bayan mutuwar mahaifiyarsa.

Marigayiyar, Mama Jummai Eli Nyame Kala ta rasu ne cikin salama a daren ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024.

Sakataren yada labaran tsohon gwamnan, Hon. Obidah Bitrus shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.